Hakkin Rai



Sai suka ce: Yaya zamu san kawukanmu. Sai ya ce: Ku yi tunani a game da idanuwanku yaya kuke gani? Da kunnuwanku yaya kuke ji? Da zukatanku yaya kuke tunani? Idan kuka san haka sai ku ji girman Allah a rayukanku, sannan sai ku kira shi zai amsa muku[6].

قالوا : وكيف نعرف نفوسنا . قال : فكروا في أعينكم كيف تبصر ؟ وفي آذانكم كيف تسمع ؟ ثم في قلوبكم كيف تفكر ؟ ؟ فإذا عرفتم ذلك شعرتم بعظمة الله في نفوسكم فدعوتموه فاستجاب لكم )

 

 Kuma idan muka leka cikin nassosi masu tsarki na shari'a zamu ga suna tabbatar da samuwar wadannan rayukan tun kafin halittar jiki, sai dai wannan mas'ala ce da aka yi sabani kanta, domin wasu suna ganin rayuka ba su riga jiki ba a samuwa, suna ganin sun samu ne sannan suka samu kamala tare da kamalar da mutum yake samu, kuma wannan ma akwai wasu ruwayoyin da suke gaskata hakan.

 

Wasu malamai sun yi bayani game da asalin rayuka da cewa tun farko aka halicce su kafin jiki, kuma suna kiran duniyarsu[7] da "Alastu", amma wasu malamai sun ture wannan da wasu hujjoji, suna masu gini a kan cewa mutum ya fara da wannan halitta ta jiki ne a cikin mahaifiyarsa, sannan sai ya samu rai yana dan wata hudu, sannan sai wannan rai din ta ci gaba da kamala, har ta samu kaiwa wani mataki mai daraja, tana mai lulluba da bargon sani a kan wani bargon, tana mai sanya tufafin ilimi a kan wani tufafin[8].

Idan mun samu gamsuwa da wannan hujja ta nazari da tunanin Sadrul Muta'allihin (k) cewa: Farkonta jiki ne, sannan sai ta samu kamalar kai wa ga narkewa cikin hasken Allah har ta koma bajiki ba. Zamu ga babu batun duniyar "barzahu" a lokacin sakkowa da gangarowar samuwa daga Ubangiji zuwa bayinsa, amma idan muka ki yarda da wannan dalili to zamu imani da samuwar rai a duniyar barzahun farko wato duniyar "Alastu".

Barzahun saukowar samuwa ta kafin samuwar duniya ke nan ta saba da wacce take a bayan mutuwa, domin na gangarowa da saukowar samuwa zuwa wannan duniya, sai da rai ta rayu a can sannan sai aka halitta jikin da aka yi mata aure da shi a wannan duniyar, sai wata ran ta auri jiki irin na mace, wata kuwa irin na namiji. Ta yadda a rai din ba su da bambanci, sai dai jiki ne ya sanya su bambanta, don haka ne sai hukunce-hukuncensu ya rataya da ta'allaka bisa nau'in jikin da ransu ta aura.

Amma barzahun bayan mutuwa ita ce wacce rayuka suke cirata zuwa gareta bayan mutuwa, duniya ce da dan Adam zai ci gaba da rayuwa a cikinta domin samun kamala, kuma dukkan surar wadannan ayyukan da ya yi a duniya zasu kasance tare da shi a wannan ranar, sai ransa ta bayyana gareshi daidai gwargwadon irin ayyukan da ya yi a wannan duniyar, don haka ne wani mutum zai tashi da sura biyu, wani da uku, ko sama da haka, sai a gan shi maciji, alade, jaki, a lokaci guda sakamakon aikin da ya yi[9].

Don haka ne ma a tayar da maganar cewa shin mutum da rai ne ko kuwa da jiki  ne, amma zamu ga wasu sun tafi a kan cewa jiki ne kawai mutum kamar 'yan mariskai (masu ganin kawai mariskan mutum biyar ne kawai suke da samuwa, amma hankali wani bayani ne nasu), da 'yan kwaminist wadanda suna cikinsu (wadanda suka kore samuwar Allah tun da ba a riskarsa da 'yan mariskai), da makamantansu duk sun tafi a kan cewa babu wani abu game da mutum sai jiki.



back 1 2 3 4 5 6 next