Hakkin Rai



Sannan sanin rayukanmu ba zai kasance kamar sauran sani ba, domin sani ne wanda ba ya daukar tsaka-tsaki balle a samu kuskure, sanin ranmu yana faruwa ne ta hanyar halartowarta[5] ga zatinmu da halittarmu, sai mu santa da dukkan samuwarm ba tare bukatar wata surar ilimi a cikin tunaninmu ba. Amma wannan sanin yana iya habbaka ya daukaka har ya kai ga sanin matsayinta da ubangijinta, da matakinta da abin da ya hau kanta, da sanin yakamata, sai ta kama hanyar kamala domin samun daraja ta koli wurin ubangijinta.

 

Don haka babban asasi shi ne mu san kawukanmu, kuma wannan shi ne mafita garemu, dukkan matsalolin mutum a duniya sun doru kan rashin sanin kansa ne, da dukkan mutane zasu san kawukansu da kowa ya tsaya haddinsa da iyakarsa, da ba a samu sabani da rikici ba, da hargowa da fitina ba su cika duniya ba. Kuma da wannan zamu san cewa lallai da gaske ne dukkan wanda ya san kansa ya san Ubangijinsa, dukkan wanda ya san Ubangijinsa ya san kansa, ba yadda za a yi mutum ya san Ubangijinsa amma bai san kansa ba, ko ya san kansa amma bai san Ubangijinsa ba.

Idan mutum ya san kansa sai ransa ta kasance ita ce mabubbugar dukkan alherai da ilimi, da hikima, kuma sai ya kakkabe dukkan jahilci da guggubinsa, da sharri da itaciyarsa. Da sanin kawukanmu ne muke karfafa, kuma da jahiltar su ne muke samun rauni, domin idan mutum ya san kansa sai ya samu lafiyar zuciya da tunani, da sha’awa, da fushi, sai ya samu karfafa su ya yi amfani da kowanne inda ya dace, amma idan ya jahilce su sai ya yi amfani da su barkatai, sai ya yi fushi mahallin hakuri, ko ya yi hakuri mahallin sha’awa, ko ya kame kansa inda ya kamata ya nuna kwadayinsa kamar tambayar abin da ya jahilta, ko ya yi kwadayi inda ya kamata ya kame kamar tambaya ko roko inda zai kaskanta.

Da sanin kansa ne zai iya samun ma’aunin rayuwa, da kuma wannan ne za a iya samun jituwa tsakanin jiki da rai domin neman cimma maslahar samuwa, da kaucewa duk wani fasadin rayuwar duniya da lahira. Idan ba a samu wannan ma’aunin rayuwa da nutsuwa ba, ba a samu da’a da biyayya ba, ba a samu dacewa da jituwa ba, sai a samu karo da juna tsakanin bukatun rai da na jiki, sai wannan ya haifar da raurawar rai da ta jiki, sai tafiyar da lamurran jiki su fuskanci matsala, daidaito kuwa ya samu rukushi.

Sanin rai yana da wasu ma'aunai da aka gindaya, idan mutum ya same su to ya san ransa. Sahabban Imam Sajjad ko Imam Bakir (a.s) sun tambaye shi cewa: Shin ba Allah yana cewa Ya ku bayina ku kira ni zan amsa muku ba. Sai ya ce: Haka ne. Sai suka ce: To me ya sa muna kiran sa dare da rana amma ba ya amsa mana? Sai ya ce: Domin ku kuna kiran wanda ba ku san shi ba. Sai suka ce: Yaya zamu san shi? Sai ya ce: Ku san kawukanku zaku san shi, sannan sai ku kira shi zai amsa muku.

 

( من عرف نفسه فقد عرف ربه ) قال صاحبي وهو يتحدث إلي : ( إن أصحاب الإمام السجاد علي بن الحسين ، أو الإمام محمد بن علي ( عليهما السلام ) سألوه : أليس الله يقول : يا عبادي ادعوني أستجب لكم . قال : صدق الله العظيم بل هو قائل ذلك . قالوا فما بالنا ندعوه ليل نهار فلا يستجيب لنا ؟ ؟ قال : لأنكم تدعون من لا تعرفون قالوا : وكيف نعرفه . قال : إعرفوا نفوسكم تعرفوه ثم ادعوه يستجب لكم

 

 



back 1 2 3 4 5 6 next