Halayen Imam Husain (a.s)



Da yanzu dukkaninmu jahannama ce makoma

Sai Imam Husain (a.s) ya ba shi dinare dubu hudu ya ba shi uzuri yana cewa:

Ka karbe ta daga gareni ina mai bayar da uzuri

Ka sani lallai ni mai tausayawa ne a gareka

Da a ce sanda ce ta wayi gari a hannunmu

Da ta zama mai maiko a gareka da maraice

Sai dai rikicewar zamani ma'abocin sabani

Ga shi tafina ta zama mai karancin amfani

Tabbas ya raya shari'ar musulunci kuma addinin kakansa (a.s) a duniya da juyin da ba shi da misali ga irinsa a duniya, kai muna iya cewa ya raya dukkan duniya ne gaba daya har zuwa ranar kiyama, kuma shi ne shugaban shahidai, kuma mafificin mutane bayan dan'uwansa (a.s).

Tarbiyyarsa: Imam Husain (a.s) ya rayu da kakansa Annabi (s.a.w) da mahaifiyarsa Azzahra'u (a.s) da mahaifinsa Amirul mu'uminin (a.s) rayuwar da dan'uwansa Imam Hasan (a.s) ya yi tare da su, na daga abin da ya tara masa abubuwan tarbiyyar Musulunci mai kaiwa ga gaci kamar dan'uwansa Imam Hasan (a.s) kuma abubuwan da – har wala yau – suka samar da mutum musulmi kamili mai tsarkin zuciya.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next