Halayen Imam Husain (a.s)



3. Ta saka musulmi yin bore da yunkuri daya bayan daya na kin jinin Umayyawa. Kuma wannan abu ya faru a cikin yunkurin Alawiyyawa.

4. Ta taimaka wajen faduwar daular Umayyawa a matsayin abu mafi muhimmanci wanda ya jawo faduwar.

Rasuwarsa: Imam Husain (a.s) ya rasu a Karbala yana wanda ya yi shahada a ranar goma ga watan Muharram shekara ta (61 bayan hijira).

Daga Cikin Shiryarwarsa:

1. Ya ku mutane. Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Wanda ya ga azzalumin mai mulki, mai halatta abin da Allah ya haramta, mai warware alkawarinsa, mai saba wa sunnar manzon Allah (s.a.w) yana yin aiki da sabo, da zalunci, a cikin bayin Allah: Bai canja abin da yake a kai ba ta hanyar aiki ko magana, to Allah yana da damar ya shigar da shi mashigarsa.

2. Allah madaukaki ya ce: (Muminai maza da muminai mata sashinsu masoya sashi ne suna yin umarni da kyakkyawan aiki kuma suna yin hani ga mummuna). Sai Allah ya fara da umarni da kyakkyawan aiki da hani ga mummuna, a matsayin wajabci ne daga gurinsa. Saboda saninsa cewar idan aka aikata shi, Kuma aka tsayar da shi to dukkan wajibabbun abubuwa ma zasu tsayu, masu sauki da masu wahala. Hakan kuwa saboda shi umarni da kyakkyawan aiki da hani ga mummuna, kira ne zuwa ga Musulunci tare da hana zalunci, da kuma saba wa zalunci, da rabon dukiyar haraji da ganimomi, da kuma karbar dukiyar shari’a daga gurarenta a bisa cancantarta.

Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com

www.hikima.org

Saturday, July 31, 2010



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next