Halayen Imam Husain (a.s)



Muslim bn Akil ya isa Kufa. kuma Imam Husain (a.s) ya fita daga Madina bayansa yana mai nufin zuwa Kufa.

Sai dai cewa a lokacin da Yazid ya san da hakan sai ya bayar da umarnin cire gwamnan Kufa da dawo da gwamnan Basara Ubaidullahi bn Ziyad a matsayin gwamna a Kufa. kuma ya ba shi gaba dayan damar da zata saka shi gyaran yanayin da ake ciki ta hanyoyi daban-daban.

A lokacin da Ubaidullahi bn Ziyad ya isa Kufa sai ya aikata wadannan abubuwa masu zuwa:

1. Neman taimakon mabiyan Umayyawa a cikin Kufa.

2. Karkato da masu neman amfani da kuma masu yin amfani da damar da suka samu su bautar da mutane domin samar da maslaha tasu su kadai.

3. Kulle mafi yawancin shugabannin kungiyar wariya da masu fada aji daga cikin mabiyansu (ta hanyar masu yi masa leken asiri da mataimakansa).

4. Ya yi amfani da siyasar rudi da ta'addanci wajen nisanta mutane daga Muslim bn Akil.

5. Ya kashe Muslim bn Akil.

6. Ya shirya mayaka domin yakar Imam Husain (a.s)… ya tattara su ne daga mabiyan Umayyawa da masu yin amfani da damar da suka samu su bautar da mutane domin samar da maslaha tasu su kadai, da masu raunin zuciya, bayan ya rude su da karin kudin da ake ba su zuwa dari dari, da kuma gaba dayan raunana da bakake wadanda suka fito saboda tsoro da kwadayi.

7. Ya kame zukatan jagororin mayakan daga cikin masu neman amfani wadanda ya rude su da dukiya da mukamai na gwamnati.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next