Annabci



A yau da kuma gobe musulmi ba su da wata mafita illa su koma ga kawukansu su yi wa kansu hukunci a kan sakacin da suka yi Su yi yunkurin gyara kansu da zuriyoyi masu zuwa ta hanyar ba su koyarwar Addininsu mai inganci domin su gusar da zalunci da ja'irci tsakaninsu.

Da haka ne kawai za su tsira daga wannan halaka mai girma kuma babu makawa daga bisani a cika kasa da adalci daidaitawa bayan an cika ta da zalunci da munanawa kamar yadda Allah (S.W.T) ya yi alkawari.

"Kuma lalle mun rubuta a littafi bayan ambato cewa kasa bayina salihai ne masu gadon ta, Lalle a cikin wannan akwai isarwa ga mutane masu ibada." Surar Anbiya'i: 105-106.

Hadisai kuma sun zo da silsila daban daban har zuwa kan Manzo (S.A.W.) da kuma Imamai (A.S) cewa: Mahadi (A.S) daga 'ya'yan Fatima (A.S) zai bayyana a karshen zamani domin ya cika duniya da daidaitwa da adalci bayan an cika ta da zalunci da rashin daidai.

Babu makawa wani Imami ya zo ya kakkabe wa Musulunci abinda aka lillika masa na daga bidi'a da bata kuma ya tserar da bil Adama, Ya kubutar da su daga abinda suka kutsa ciki na daga fasadi gama gari da zalunci mai dorewa, da kiyayya mai ci gaba, da izgili da koyarwar kyawawan dabi'u da ruhin dan Adamtaka. Allah ya gagagauta bayyanarsa ya saukake hanyar bayyanarsa.

Mai Shara'anta Musulunci

Mun yi imani da cewa ma'abucin sakon Addinin Musulunci shi ne Annabi Muhammadu dan Abdullahi kuma shi ne cikamakin Annabawa shugaban Manzanni kuma mafificinsu baki daya, kamar kuma yadda shi ne shugaban dan Adam baki daya. Babu wani mai falala da ya yi daidai da shi, babu wani da ya yi kusa da shi a karimci babu wani mai hankali da zai yi kusa da shi a hankali babu wani kamar shi kuma a kyawawan dabi'u kuma shi yana kan manyan kyawawan dabi'u, Allah Ta'ala Yana cewa: "Lalle  kana kan manyan halayen kwarai masu girma." Surar 11- kalam: 4. Wannan kuwa tun daga farkon tasowarsa ne har zuwa ranar tashin Alkiyama.

Amirul muminina Aliyyu Dan Abi Talib (A.S.) ya siffanta shi a daya daga cikin hudubobinsa yana cewa: "Ya zabe shi bishiyar Annabawa da fitila mai haske da kuma mai tsororuwar daukaka da mafi darajar gurare, da fitilun haskaka duffai da kuma mabubbugar hikima".

Daga cikin wannan hudubar har ila yau Amirul Muminina (A.S) yana cewa: "Likita mai zazzagawa da maganinsa ya shirya kayan aikinsa yana amfani da su duk lokacin da bukata ta kama wajen warkar da makantattun zukata, da kuraman kunnuwa, da bebayen bakuna, yana bibiyar guraren gafala da maganinsa da kuma guraren rudewa, ba su yi amfani da hasken hikima ba, ba su kunna kyastu makoyar ilimi ba, su sun zamanto kamar dabbobi masu kiwo da duwatsu masu tsauri." (Nahajul Balagha Huduba ta 108).

Alkur'ani Mai girma.

Mun yi imani cewa Alkur'ani wahayin Ubangiji ne da ya sauko daga Allah a harshen AnnabinSa, akwai bayanin kome da kome a cikinsa shi ne Mu'ujiza madawwamiya wadda ta gagari bil Adama wajen karawa da ita a fasaha da azanci, abinda ya kunsa na daga hakika da sannai madaukaka, jirkita ko canji ko karkacewa ba sa shafar sa, Allah Ta'ala yana cewa:

"Mu Mu ne Muka saukar da ambato kuma Mu gare shi lalle masu kariya ne". Surar Hijri: 9.

Alkur'anin da ke hannunmu wanda ke karanta shi a yau shi ne wanda aka saukar wa Annabi (S.A.W) duk kuma wanda ya yi da'awar sabanin wannan to shi mai kage ne, ko mai rikitarwa ko mai kuskure ne dukaninsu kuma ba a kan shiriya suke ba, domin shi Alkur'an zancen Allah ne wanda Karya ba ta zuwa masa ta gaba gare shi ko kuma ta bayansa. Surar Fusilat: 42.

Daga cikin dalilan da ke tabbatar da mu'ujizarsa akwai cewa duk yayin da zamani ya dada tsawo ilimi da fasaha kuma suka dada ci gaba shi yana nan daram a kan abubuwan da yake kaddamarwa da daukarkar manufa da abubuwan da ya kunsa na ra'ayoyi babu wani kuskure da ke bayyana daga cikinsa dangane da tabbatattun matsayi na ilimi kamar kuma yadda ba ya taba kunsar tawaya game da falsafa ta hakika da yakini sabanin littafan da malamai da manyan masanan falsafa kome matsayin da suka kai kuwa a fagen ilimi da kuma amfani da kwakwalwa da tunani. Domin duk yayin da bincike ya ci gaba to yakan bayyana a sarari cewa rarrauna ne ko sabo ne ko kuma kuskure hatta a gurin manyan masana falsafar kasar girka kamarsu Sakarot da­ Aplato da Arostatle wadanda kowa da kowa daga cikin wadanda suka zo daga bayansu suka yi musu shaida da cewa su ne iyayen ilimi da kuma amfani da kwakwalwa.

Kazalika mun yi imani da mutunta Alkur'ani mai girma da daukaka shi a magana da kuma a aiki. Bai halatta a najasta koda kalma guda a cikinsa wadda aka dauka cewa yanki ne daga cikinsa da kuma nufin cewa daga cikinsa take, Kamar kuma yadda bai halatta ba ga wanda ba shi da tsarki ya shafa kalmominsa ko harrufansa: "Babu mai shafa shi sai wadanda suke tsarkakakku". Surar Waki'a: 79.

Sawa'un sun kasance suna da babban kari ne kamar janaba ko haila ko jinin biki da makamantansu, ko kuma karamin kari koda ma barci ne kuwa sai dai bayan yin alwala ko kuma yin wannan a bisa asasin filla-fillan bayanan da ke cikin littafan fikihu.

Haka nan bai halatta a kona su ba, bai halatta wulakanta shi ba, koda ta wace fuska ne kuwa da yake sananne a tsakanin mutane kamar jefarwa, ko sanya masa kazanta, ko shurin sa da kafa, ko sanya shi a guri wulakantacce, Idan da wani zai wulakanta shi da gangan ko tozarta shi da aikata daya daga cikin wadannan abubuwan da muka ambata da makamantansu to shi ya shiga cikin masu karyata Addinin Musulunci da abubuwan tsarkakewarsa, kuma abin hukuntawa ne da ficewa daga Addini da kafircewa ga Ubangijin talikai.

 



back 1 2 3 4 5 6 7