Annabci



Ma'anar wajibi a nan ba wai tana nufin cewa wani za a umarce shi da aikata haka ba ne har ya zama tilas a kansa ya yi wa wanda Ya yi umarni biyayya! Allah ya daukaka ga haka ma'anar wajibi a nan tamkar ma'anar fadin da ake yi ne cewa shi Allah wajibin samuwa ne wato ba zai taba koruwa ba, ba zai taba yiwuwa a raba shi da samuwa ba.

Mu'ujizar Annabawa

Mun yi imani da cewa lalle Ubangiji (S.W.T) tunda yake sanya wa bayinsa mai shirya da kuma Manzo to babu makawa ya sanar da shi gare su, ya kuma nuna musu ko wane ne shi a ayyane. Wannan kuwa ya takaita ne a kan sanya musu wani dalili da kuma kafa musu hujja a sakon domin cika tausasarsa da kuma kammala rahamarsa.

Allah Ta'ala Yana cewa:

"Manzanni masu bushara da kuma gargadi domin kada mutane su zama suna da wata hujja a gurin Allah  bayan Manzanni kuma Allah mabuwayi ne Mai hikima." Surar Nisa'i: 165.

Wannan, kafa hujjar kuwa babu makawa ya zamanto irin wanda ba ya samuwa sai daga mahaliccin halittu mai sarrafa samammu wato ya zama abinda ya gagari kudurar dan Adam ya sanya shi a hannun shi Manzon mai shiryarwa domin ya zamanto an san shi da shi kuma mai shiryarwa zuwa gare shi, wannan dalili da hujja shi ake kira mu'ujiza wato gagara badau saboda kasancewarsa ya gagari dan Adam ya yi gasa da shi ko kuma ya kawo makamancinsa.

Kamar yadda babu makawa ga Annabi ya zo da mu'ujiza ya bayyana ta ga mutane domin ya kafa musu hujja haka nan babu makawa wannan mu'ujizar ya nuna ta kuma yadda za ta gagari malamai da kuma kwararrun zamaninsa ballantana kuma sauran mutane, tare kuma da danganta wannan mu'ujizar da ikrarin Annabci daga mai mu'ujizar, saboda kasancewarsa yana da sadarwa ruhi da wanda yake jujjuya halittu.

Idan wannan ya tabbata ga mutum, bayyanar mu’ujiza wadda ta saba wa al’ada, ya kuma yi da'awar Annabci da sako, to a lokacin sai ya zamanto abin gaskatawar mutane a kiran da yake yi tare da yin imani da sakon nasa da bin maganarsa da umarninsa, sai wanda zai gaskata shi ya yi imani da shi wanda zai ki kuma ya kafirce masa.

Wannan shi ne abinda ya sa muka ga cewa mu'ujizar kowane Annabi ta dace da ilimi da kuma fasahar zamaninsa, mu’ujizar Annabi Musa ita ce sanda wanda ke hadiye sihiri da abinda suke yin baduhunsa saboda kacancewar sihiri a zamaninsa shi ne fannin fasaha da yake mashahuri, yayin da sandan ya zo sai dukan abinda suke aikatawa ya baci suka san cewa lalle wannan abu ne da ya fi karfinsu kuma ya dara irin fannin fasaharsu. lalle wannan yana daga cikin abubuwan da dan Adam ya gaza ya kawo shi kuma kwarewa da ilimi sun gajiya a gabansa. Allah Ta'ala yana cewa:

"Kuma sai muka yi wahayi ga Musa kan cewa jefa sandarka sai ga shi tana hadiddiye abubuwan da suke kirkirawa. Kuma gaskiya ta tabbata abinda suke aikatawa kuma ya baci, Sai aka yi rinjaye a nan sa'annan suka koma suna kaskantattu, Kuma aka kifar da masu sihirin suna sujada." Surar A'araf; 117-120.

Hakanan mu'ujizar Annabi Isa (A.S.) ita ce warkar da makafi da masu albaras da kuma raya matattu saboda shi ya zo ne a lokacin da likitancin ne yake afannin fasahar kwarewar da ke tsakanin mutane kuma akwai malamai likitoci da suke su ne manyan bokaye da iliminsu ya gaza kafada da kafada da abinda Annabi Isa (A.S.) ya zo da shi. Allah ta'ala Yana cewa:



back 1 2 3 4 5 6 7 next