Annabci



 "Kuma Manzo zuwa ga Bani Isra'ila cewa lalle ni na zo muku da aya daga Ubangijinku ni ina halitta muku daga laka abinda yake kamar surar tsuntsu kuma in hura a cikinsa ya zamanto tsuntsu da izinin Allah kuma ina warkar da makaho da mai albaras kuma ina raya mamata da izinin Allah  kuma ina ba ku labarin abinda kuke ci da wanda kuke taskancewa a gidajenku lalle a cikin wannan akwai aya gare ku idan kun kasance muminai." Surar AI- Imran: 49.

Mu’ujizar Annabinmu madawwamiya ita ce Alkur'ani saboda shi ya zo ne a lokacin ma'abuta ilimin balaga su ne kan gaba a tsakanin mutane inda ya kure su da balagarsa da bayaninsa. Duk da fasaharsu da bayaninsu sai da Alkur'ani ya kaskantar da su ya rikitar da su ya fahintar da su cewa su ba za su iya fito na fito da shi ba. Don haka suka sallama masa rinjayayyu bayan sun gaza kasawa da shi, suka ma gaza isa ga kurar da ya tile su da ita ya wuce ya barsu.

Allah Ta'ala yana cewa:

 "Kuma idan da mutane da Aljannu za su taru a kan su zo da kwatankwacin wannan Alkur'anin to da ba za su zo da makamancinsa ba koda kuwa sashensu na taimakon sashe." Surar Isra'i: 88.

Kalubalantar su da ya yi kan cewa su kawo sura goma suka kasa na tabbbatar da cewa lalle ya gagare su. Allah Ta'ala Yana cewa:

"Ko suna cewa shi ne ya kage shi ne ka ce to ku zo da surori goma makamantansa kagaggu kuma ku kira duk wanda za ku iya wanda ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya" Surar Hud: 13

Sa'an nan kuma ya sake kalubalantar su kan su kawo sura guda kamar sa suka gaza. Allah Ta'ala Yana cewa:

 "Kuma idan har kun kasance a cikin kokwanto daga abinda muka saukar to ku zo da sura guda kamar sa kuma ku kira shaidunku da ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya". Surar Bakara: 23

Allah Ta'ala Yana cewa:

 "Ko suna cewa ya kage shi ne ka ce ku zo da sura guda kamarsa kuma ku kira duk wanda za ku iya koma bayan Allah  in kun kasance masu gaskiya". Surar Yunus: 38.



back 1 2 3 4 5 6 7 next