Allah Madaukaki



Mafi girman siffar da take fara zuwa a jerin sunayensa ita ce kadaitawa, domin ya wajaba a kadaita Allah ta kowace fuska kamar yadda ya wajaba a kadaita shi a zatinSa, da samuwarsa, da siffofinsa da cewa siffofinsa su ne ainihin zatinsa kamar yadda bayani zai zo game da hakan.

Haka nan wajibi ne a kadaita Shi a bauta, bai halatta a bauta wa waninsa ba ta kowace fuska, kamar yadda bai halatta ba a hada Shi da wani abu a nau’o’in ibada, wajiba ce ko wadda ba wajiba ba, a salla ne ko kuma waninta na daga ibadoji. Duk wanda ya yi shirka ya hada wani da Shi a ibada to Shi Mushiriki ne, kamar wanda yake riya a ibadarsa yake neman kusanci zuwa ga wanin Allah (s.w.t), hukuncinsa da wanda yake bauta wa gumaka daya ne babu bambanci a tsakaninsu.

Wasu mutanen sun so su kore musulunci daga dukkan wanda yake ziyarar kaburbura, da tawassuli da waliyyan Allah, da da’awar cewa shirka ne. sai dai lamarin ba haka yake ba, domin ziyartar kaburbura da gudanar da bukukuwa ba sa daga cikin nau’in neman kusanci da wanin Allah a ibada. Wadannan ba komai ba ne sai wani nau’i na aiki domin samun kusanci zuwa ga Allah (s.w.t) ta hanyar kyawawan ayyuka, kamar neman kusanci gare shi ta hanyar gaishe da maras lafiya, da kai jana’iza, da ziyartar ‘yan’uwa, da taimakon talaka.

Don zuwa gaishe da maras lafiya Shi a kan kansa kyakkyawan aiki ne wanda mutum kan samu kusanci da Allah ta hanyarsa, ba neman kusanci da maras lafiyar ba ne da zai sanya aikinsa ya zama bauta ga wanin Allah (s.w.t) ko kuma shirka a bautarSa, haka nan sauran ayyukan ibada. Dukkan wadannan ayyukan ba komai ake nufi da su ba sai rayar da al’amuran Allah da waliyyansa, da sabunta tunawa da su, da kuma girmama alamomin Addinin Allah a tare da su “Wannan, duk wanda ya girmama alamomin addinin Allah to lalle wannan yana daga cikin ayyukan takawar zukata”. Surar Hajj: 32.

Daya daga cikin mafi girman lamari a bahasin sanin Allah madaukaki shi ne na siffofinsa tsarakaka; da farko dai ana kasa wadannan siffofi zuwa siffofi tabbatattu na kamala da (jamal) kamar ilimi, da iko, da wadata, da nufi, da rayuwa, wadanda suke su ne ainihin zatinSa.

Wasu sun dauka wadannan siffofin su daban ne, kuma kari ne kan samuwar zatin Allah, ta yadda su ma suna da tasu samuwar ta daban. Sai dai mu muna cewa wadannan siffofi ba kari suke ba a kan zatinSa, kuma ba komai ne samuwarsu ba sai samuwar zatin Allah, kudurarsa ta fuskacin rayuwarsa ita ce ainihin rayuwarsa, rayuwarsa ita ce kudurarsa, Shi mai kudura ne ta fuskacin kasancewarsa rayayye, kuma rayayye ta fuskacin kasancewarsa mai kudura, babu tagwayantaka (biyuntaka) a siffofinSa da samuwarsa, haka nan yake a sauran siffofinsa na kamala.

Amma wadannan siffofin sun sassaba a ma’anoni, ba a hakikanin samuwarsu ba, domin da sun kasance sun sassaba a samuwarsu, da an sami kididdigar Ubangiji, kuma da ba a sami kadaitaka ta hakika ga Ubangiji ba, wannan kuwa ya saba wa Akidar Tauhidi.

Sannan akwai wasu siffofi masu nuna aikin ubangiji kamar[2] halittawa, arzutawa, gabatuwa, da kuma samarwa. Wadannan, duk suna komawa ne a bisa hakika zuwa ga siffa guda ta hakika, wato siffar nan ta tsayuwa da al’amuran halittarsa, ita siffa ce guda daya wacce ake fahimtar irin wadannan siffofi daga gareta gwargwadon tasirori da ayyukansa ga bayinsa.

Amma siffofin da ake kira salbiyya wato korarru; da aka fi saninsu da siffofin Jalal, dukkansu suna komawa ne zuwa kore abu daya, wato kore nakasa[3] daga ubangiji ko duk wata tawaya kamar jiki, sura, fuska, motsi, da rashin motsi, nauyi, da rashin nauyi, da sauransu.

Shugabanmu Amirul Muminin (a.s) ya yi nuni ga hakikanin siffofin Allah madaukaki yana mai cewa: Cikar tsarkake wa gareshi kuwa shi ne kore siffofi (n halitta) gare Shi[4], saboda shaidawar dukkan abin siffantawa cewa ba shi ne siffar ba, da kuma shaidawar kowace siffa cewar ba ita ce abin siffantawar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah (da irin wadancan siffofi) to ya gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi, wanda ya tagwaita Shi kuwa ya sanya Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi, wanda kuwa ya jahilce shi zai yi nuni gareshi, duk wanda kuwa ya nuna shi ya iyakance shi, wanda kuwa ya iyakance shi to ya kididdiga shi, wanda ya ce: A cikin me yake? To ya tattaro shi a wani wuri, wanda ya ce: A kan me yake? To ya sanya shi ba ya wani wurin[5].



back 1 2 3 4 next