Allah Madaukaki



Da sunan Allah madaukaki

Kalmar “Allah” suna ne madaukaki na mahallici wanda wasu suka tafi a kan cewa shi ne suna mafi girma.

Allah yana da siffofi da ayyuka, wadannan siffofin nasa su ba irin na sauran samammu ba ne, domin shi siffofinsa azali ne wadanda suke tare da shi tun azal, amma sauran halittu siffofinsu suna bujuro musu ne.

Sai dai tun farko yana da kyau mu sani cewa sanin Allah madaukaki yana bukatar ayyana hanyar saninsa ga mai rubutu, domin wani yakan yi bayanin Sanin Ubangiji madaukaki ta hanyar Falsafa, wani kuma ta hanyar Irfani, da makamantansu. Amma mu a nan muna son yin wani gajeren bayani game da Allah madaukaki ta hanyar hankali da shara’a ne.

Da farko dai mu sani cewa Allah ya yi mana baiwar da babu wani mai rayuwar a doron kasa da ya same ta. Ya yi mana falalar da baiwar karfin tunani da kyautar hankali, don haka ne ma ya umarce mu da mu yi tunani a kan halittarsa mu kuma yi duba a cikin a alamomin ayyukansa, mu yi la’akari a cikin hikimarsa da kuma kyautata tafiyar da al’amuranSa a ayoyinsa a cikin duniya baki daya da kuma a kawukanmu, Allah Madaukaki yana cewa: “Zamu nuna musu ayoyinmu a sasannin duniya da kuma a kawukansu har sai ya bayyana gare su cewa hakika Shi gaskiya ne”. Surar Fussilat: 53. Kuma Ya zargi masu bin iyayensu -a akida- da fadinsa: “Suka ce mu dai kawai muna bin abin da muka samu iyayenmu a kai ne, ashe koda ma iyayen nasu sun kasance ba su san komai ba”. (Surar Bakara: 170). Kamar kuma yadda ya zargi wadanda suke bin zato kawai da shaci-fadi cikin duhu da cewa: “Ba komai suke bi ba sai zato”. Surar An’am: 116.

Wannan ni’imar ta hankali ita ce ta wajabta mana yin bincike domin sanin Allah madaukaki, ta yadda muna iya cewa dokokin hankali suna tilasta mana hakan. Don haka ne abin da ya zo a cikin Kur’ani na kwadaitarwa a bisa tuntuntuni da bin ilimi da sani ya zo ne don karfafa wannan `yanci na dabi’ar halitta ta hankali.

Kuma babban kuskure ne ga wani mutum ya ya yi wa kansa saki-na-dafe a kan al’amuran Akida, ko kuma ya dogara da wasu mutane, ya wajaba ne a kansa ya karfafa kan yin bincike ya yi tunani ya yi nazari ya yi bincike a kan asasin shika-shikan Akidarsa, ya san ubangijinsa[1].

Don haka a kanmu akwai nauyin wajabcin bincike da neman sani a kan shika-shikan akida, bai halatta ba a yi koyi da wani a cikinsu ba, kuma na farko shi ne ubangiji madaukaki. Wannan wajabcin saninsa bai samo asali daga nassosin addini ba duk da ya inganta a karfafe shi da su bayan hankali ya tabbatar da shi.

Sau da yawa marubuta sukan kawo sunayen Allah da siffofinsa kamar haka: Allah madaukaki daya ne makadaici, babu wani abu kamarsa, magabaci ne, bai gushe ba kuma ba ya gushewa. Shi ne na farko kuma Shi ne na karshe, Masani, Mai hikima, Adali, Rayayye, Mai iko, Mawadaci, Mai ji, Mai gani. Ba a siffanta Shi da abin da ake siffanta halittu da shi, shi ba jiki ba ne, kuma ba sura ba ne, ba Shi da nauyi ko sako-sako, ba Shi da motsi ko sandarewa, ba Shi da guri ba Shi da zamani, kuma ba a nuni zuwa gare Shi, kamar yadda babu tamka gare Shi, sannan ba a iya riskarsa da wasu mariskai.

Duk wanda ya ce ana kamanta shi da halittarsa, kamar ya suranta fuska gare Shi da hannu da idaniya, ko cewar Yana saukowa zuwa saman duniya, ko yana bayyana ga ‘yan aljanna kamar wata ko kuma makamantan wannan, to yana matsayin jahilci hakikanin mahaliccin da ya tsarkaka daga nakasa, kai dukkan abin da muka bambance shi da tunanin kwakwalwarmu da sake-saken zukatanmu a mafi zurfin ma’anarsa, to shi abin halitta ne kamarmu, mai komawa ne zuwa gare mu, kamar yadda ya zo daga Imam Bakir (a.s).



1 2 3 4 next