Bincike Kan Addini



“Wannan kuwa domin Allah bai kasance yana canja wata ni’ima da ya ni’imtar da ita ga wasu mutane ba face sai sun canja abin da yake ga kawukansu”. Surar Anfal 53. Da fadinsa “Kuma wannan ita ce sunnar Allah a halittunsa cewa tabbas masu laifi ba sa cin rabauta”. Surar Yunus: 17. Da fadinsa madaukaki: “Kuma Ubangijinka bai kasance mai halakar da alkaryu ba bisa zalunci alhali mutanenta suna masu gyara”. Surar Hudu: 117.

Da fadinsa: “Kuma haka nan kamun Ubangijinka yake idan ya kama alkarya alhali tana azzaluma lalle kamunsa mai radadi ne mai tsanani”. Surar Hudu: 102.

Ta yaya ake sauraron Addinin musulunci ya tayar da al’umma daga dogon baccinta, alhali kuwa shi a wajanta kamar tawada ce a kan takarda da ba a aiki da mafi karanci daga koyarwarsa. Imani, da amana, da gaskiya, da tsarkin niyya, da kyautata mu’amala, da sadaukarwa, da musulmi ya so wa dan’uwansa musulmi abin da yake so wa kansa, da makamantansu, tun farkon assasa Addinin musulunci musulmi sun yi bankwana da su tun da can har zuwa yau. Kuma duk sanda zamani ya ja gaba sai mu same su suna kara rarraba jama’a-jama’a da kungiya-kungiya, suna kifuwa da goggoriyo a kan duniya, suna ta fagamniya a cikin duhu, sashensu na kafirta sashe da wasu ra’ayoyi gagara fahimta, ko kuma a kan wasu al’amura da babu ruwansu a ciki, suka shagaltu ga barin asasin Addini da maslaharsu da maslahar al’ummarsu, da fadawa cikin jayayya game da halittar Kur’ani ko rashin kasancewarsa abin halitta, da batun narkon azaba da Raja’a, da kuma cewa aljanna da wuta halittattu ne a halin yanzu ko kuma za a halicce su ne nan gaba.

Sai ga shi a yau yammacin duniya wayayye, fadakakke, ya samu damar mulkin mallaka a kan wani yanki da yake na musulmi, su kuwa sun yi zamansu cikin gafala da rafkanwa yadda har ya iya jefa su cikin mummunan halin da Allah ne kadai ya san iyakarsa da lokacin karewarsa. Allah madaukaki yana cewa: “Kuma Ubangijinka bai kasance yana halakar da alkaryu ba bisa zalunci alhali mutanenta suna masu gyara”. Surar Hudu: 117.

Don haka musulmi ba su da wata mafita sai koma wa kawukansu su yi wa kansu hisabi a kan sakacin da suka yi, su yi yunkurin gyara kawukansu da zuriyoyi masu zuwa, ta hanyar ba su koyarwar Addininsu mai inganci domin su gusar da zalunci da ja’irci tsakaninsu.

Da haka ne kawai zasu tsira daga wannan halaka mai girma, kuma babu makawa bayan nan su cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci kamar yadda Allah (s.w.t) ya yi musu alkawari. Kuma kamar yadda ake saurare daga addininsu da yake shi ne cikon addinai da ba a kaunar wani gyara na duniya ko lahira sai da shi[12].

Babu makawa wani Imami ya zo ya kakkabe wa musulunci abin da aka lillika masa na daga bidi’o’i da bata kuma ya tserar da ‘yan Adam, ya kubutar da su daga abin da suka kai matuka gareshi na daga fasadi, da zalunci mai dorewa, da kiyayya mai ci gaba, da izgili da halaye nagari da ‘yan‘adamtaka. Allah ya gaggauta bayyanarsa ya saukake mafitarsa.

Cibiyar Al’adun Musulunci

www.hikima.org

Hafiz Muhammad Sa’id



back 1 2 3 4 5 6 next