Bincike Kan Addini



Sai mu ce: Addini shi doka ce ta Allah da take tsara rayuwar dai-daikun mutane da jama’a gaba daya, domin kai wa ga kamala da daukaka a dukkan fagagen rayuwa masu muhimmanci da suka shafi rayuwar mutum wanda ya hada da;

1-      Gyara Masa Tunani Da Akida Da Tsarkake Shi Daga Camfi Da Surkulle:

Addini yana fassara mana hakikanin yadda samuwa take da kuma cewa akwai mai samarwa, masani, mai iko, da ya halicci dukkan halitta da kuma asalinta, da iyakance asalin da dokokinta. Kamar yadda yake fassara ma’anar rayuwar mutum da cewa ba haka nan kawai ta ke ba, ba a halicci mutum don wasa ba, sai domin wani hadafi babba da zai kai zuwa gareshi ta hanyar biyayya ga koyarwar da annabawa da masu shiryarwa suka zo da ita daga Allah.

2-     Karfafa Asasin Kyawawan Dabi’u

Akida ta addini ita ce madogara mai karfi ta asasin kyawawan dabi’u, domin sanya dokoki da daure mutum da su yana sanya masa wahala da kuma bukatuwa zuwa ga juriya da mutum zai yi, kuma jure su ba ya yiwuwa sai da imani da Allah da zai saukaka su, da kuma kwadaitar da mutum zuwa ga sadaukar wa ta hanyar gaskiya da adalci da taimakon raunana.

3-     Kyautata Alakar Zamantakewa:

Akidar mutum ta addini tana karfafa asasin zamantakewa domin zata sanya mutum ya zama mai addini da kuma lizimtar takalifi da bai halatta ya saba masa ba kamar sadar da zumunci da girmama iyali da sauransu.

4-     Jefar Da Bambance-bambance:

Addini yana ganin mutane dukkansu halittu ne na ubangiji guda daya, kuma dukkansu a wajan Allah daya ne ba bambanci tsakanin balarabe da ajami da fari da baki[6].

Wadannan al’amura guda hudu suna nuna mana muhimmanci mai girma a fili da addini yake da shi, kuma bayan haka ba zai yiwu ga wani ba ya bar addini domin gudun kada wani nauyi ya hau kansa ko son hutu da holewa, ko kuma domin addini yana sanya wa mutum dokoki da zasu hana shi aiwatar da abin da ransa ta ga dama.



back 1 2 3 4 5 6 next