Bincike Kan Addini



 Da sunan Allah madaukaki

Bayani kan Addini wani abu ne da aka samu sabani mai tsanani tsakanin ma’abota tunani a kansa, sai dai mu zamu takaita game da wasu bayanai masu sauki da sukan iya ba mu ma’anar da ta fi kowacce cika.

Addini a luga: biyayya: Allah madaukai yana cewa: “Biyayya gaba daya tasa ce”[1]. Ma’ana: biyayya da da’a dawwamammiya tasa ce”.

Haka nan yake cewa: “Ba sa biyayya da biyayya ta gaskiya”[2].

Kuma kalmar addini ta zo da ma’anar sakamako kamar fadinsa madaukaki: “Mamallakin ranar sakamako”[3].

Don haka kalmar addini a luga tana nufin sakamako ko biyayya[4].

 Addini a isdilahi: shi ne imani da mahaliccin halitta, da mutum, da kuma koyarwa, da ayyukan da suke da tushe da asasi daga karkashin wannan imanin.

Saboda haka ne ma ake kiran wadanda ba su yi imani da mahalicci ba da marasa addini[5].

 

Wasu suna iya cewa menene amfanin addini? Me zamu samu daga gareshi? Kai wasu ma suna da’awar cewa akwai cutuwa a addini.



1 2 3 4 5 6 next