Hanyoyin Tarbiyya



f. Yi masa bayanin musulunci, da hikimarsa, da koyarwarsa mai kima da muhimmanci, domin gudun kada ya taso yana jahiltar addininsa. Kamar yadda sanar da shi Ubangjinsa ya zama wajibi na farko da za a ilmantar da shi a rayuwarsa. Sannan sai abin da zai biyo baya na sanar da shi hukunce-hukuncen addininsa, da kyawawan halayen musulunci da kimar da suke da ita, da koyar da shi al'adu na gari, da tarbiyyantar da shi kan kokarin aiki da su.

6- Sanya lura da karfafawa a kan babbar gudummuwar da telebishan, da radiyo, da mujallu, da kissoshi masu hoto, da labaru zasu iya bayarwa wajan tarbiyyar yara da gina su[8]. Wannan wani lamari ne da makarantu, da iyaye, da kafafen isar da sako, ya kamata su himmantu da su.

7- Duba zuwa ga tarihin gidaje na gari, muna da babban misali game da kissoshin "Gidan Abrar" wato gidan Ahlul Baiti (a.s) da ya hada da Sayyidi Ali (a.s) da Fadima (a.s) da ‘Ya’yansu Hasan da Husaini (a.s).  Da koyar da kissarsu da ta zo a cikin surar Insan, wacce take koyar da mu sadaukarwar da suka yi, da alwashin yin azumi da suka yi, da kuma sadakar da suka yi da abin da zasu sha ruwa da shi karshen kowane azumi har kwana uku a jere; ga maraya, da miskini, da kuma ribataccen yaki[9], domin karanta irin wadannan kissoshi zai sanya mana daukar ilimi da darussa masu yawa game da yadda ya kamata salihin gida mai tarbiyya ya kasance.

Mai son samun cikakkun bayanai kan alakar iyaye da ‘ya’yansu sai ya nemi littafinmu mai suna “Alakar Iyaye Da ‘Ya’yansu”.

Hafiz Muhammad Sa'id

www.hikima.org

hfazah@yahoo.com

Sunday, November 15, 2009


[1] Fikihus sunna, sayyid sabik, babin: zabar miji.

[2] Fikihur Ridha, ibn babawaih, shafi: 234.

[3] Alhada’ikun nadhira, al’muhakkikul baharani, shafi: 195.

[4] Almahasin, j 2, ahmad bn muhmmad bn Khalid albarki, shafi: 333.

[5] Attuhfatus Saniyya, Sayyid Abdullahi Aljaza'iri, shafi: 297.

[6] Surar Yusuf: 12.

[7] Kashful Kafa’, Al’ajiluni, j 1, h 255, shafi: 94 – 95.

[8] Ilajul amradhul akhlakiyya, bugu na biyu, shaikh abdurrasul Ali anuz, mai yadawa: maktabar dawari, shafi: 42 - 44.

[9] Insan: 8.

 



back 1 2 3 4 5