Hanyoyin Tarbiyya



Wasu Bayanai: A nan muna son mu yi nuni da wasu daga cikin hanyoyin tarbiyyar yara cikin wasu bayanai da suke kunshe a cikin littattafan masana tarbiyyar yara a dunkule kamar haka:

Na daya: Ta hanyar bayar da labarai da kissoshi, misali na san mahaifinmu ya taba ba mu labari kan hadarin wulakanta mutane domin ba ka sani ba ko wani waliyyi ne ka wulakanta sai Allah (s.w.t) ya yi maka azaba, wannan kuwa ba na mantawa a shekarar 1983 ne, sai ya zamanto idan mun ga wani yana tsokanar wani mutum saboda tawaya ta halittarsa mukan gaya masa ba ka sani ba ko waliyyi ne.

Yaro mutum ne mai son tarihi da labarai, kuma a lokacin da nake koyarwa a Furamare da kuma Sakandare na ga amfanin haka sosai, ta yadda soyayya da kaunar juna ta faru tsakanina da dalibai, har ma koda a kan hanya ne wani ya gan ni yakan taho a guje ya ce: Gobe tarihi fa za a yi mana.

Babu wata hanya da tafi a wurin tarbiyyantarwa kamar hanyar tattaunawa, a cikin wadannan hanyoyin kuwa duk babu wacce ta kai hanyar bayar da kissoshi, da hikayoyi, da tarihi.

Ta hanyar labaru kakan iya koya wa yara jarumtaka da girmama mutane, da son al’ummarsu, da neman kawo gyara cikinta, da jin lallai dole su dauki nauyin isar da sakon Allah ga mutanensu, da son kyauta da taimaka wa marasa shi, da nisantar rowa, da sadaukarwa don mutanensu, da son iyaye da rashin saba musu, da kaskantar da kai ga mutane, da sanin Allah.

Na biyu: Abokantaka da yaronka ta yadda zaka iya yi masa tasiri ta hanyar hira da shi da nuna masa shi ma mutum ne mai iya tunani, har ma ka dauki shawara daga gare shi ta yadda zai ji cewa shi ma mutum ne kamili.

Rashin wannan ya sanya yara suna jin su tauyayyu ne, kamar dai yadda al’adu suka nuna mata ne a cikin al’ummu har wannan ya yi musu tasiri a tunaninsu, haka nan suka dauki yara a matsayin kaskantattu, aka yi musu irin wannan mu’amala har ya yi musu tasiri, shi ya sa sau da yawa sukan taso ba su san al’ummarsu ko duniyar da suke cikinta ba.

Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: “Yaro a shekara bakwai na farko shugaba ne kuma sarki, a shekara bakwai kuma bawa ne ribataccen yaki, a shekara bakwai kuma dan’uwa ne kuma waziri”[7]. Wannan Hadisi yana nuna mana shekara ishirin da daya da zaka yi tare da yaro, da irin mu’amalar da zaka yi da shi a kowacce daga shekaru bakwai.

Na uku: Koyar da yaro kada ya cuci wani ta hanyar sanya tausayin al’umma a zuciyarsa kuma da koya masa kada ya karbi a zalunce shi, da tausaya wa wanda aka zalunta da nakasassun mutane kamar mai bara da talaka, wannan yana iya faruwa ta hanyar ba su labarai da tarihi na magabata domin ya yi tasiri a kansu.

Na hudu: Sanar da yaro tarihi da labaran yadda kasarsa take da kuma abin da kakanninsu suke a kai na alheri da kwadaita masa wannan, da sanar da shi kabilun kasarsa da hakkokinsu a kansa, da koya masa yadda zai kiyaye hakkin sauran abokan zamansa na kasarsa musulminsu da wadanda ba musulmi ba.



back 1 2 3 4 5 next