Hanyoyin Tarbiyya



1- Dasa wa yaro jin nutsuwar zuci, da kama hannunsa domin daukaka matsayinsa, wannan kuwa yana iya kasancewa ne ta hanyar rashin wulakanta shi, da sanya masa jin daukaka da kamala ko rashin nuna masa gazawarsa. Don haka abin da ya kamata shi ne: a rika tattaunawa da shi, da neman shawararsa da nuna masa inda ya samu rauni, domin ya taso mutum mai dauke da jin cewa zai iya kasancewa jagora a kowane fage.

2- Rashin kallafa wa yaro abin da ya fi karfinsa, ko kuma ayyukan da ba ya son su, domin gudun kada ya gajiya ya kasa, wannan kuma yana iya janyo masa jin kasawa da rushe himmarsa.

3- Dada wa yaro kaimi domin ya zama wani babban mutum ta hanyar girmama masa manyan mutane da suka gabata ko rayayyu, da yi masa bayanin sirrin abin da ya sanya suka zama manyan mutane masu daraja, da kuma hanyoyin da suka bi domin kai wa ga wannan matsayin.

4- Kula da yaro domin kada girman kai da ruduwa da kansa su same shi domin yana ganin ya fi sauran abokansa kokari a karatu, da koya masa siffofin dabi’u kyawawa da ya kamata ya siffantu da su, da nuna masa wadannan ni’imomi da yake da su daga Allah ne kuma shi zai godewa.

5- Yi wa yaro bayanin abin da al’ummarsa take ciki dalla-dalla, da nuna masa yadda zai bayar da tasa gudummuwa domin kawo ci gaban al’ummarsa ta hanyar:

a. Samar masa akida ta gari da zai doru a kanta.

b. Bayanin gudummuwar da al’ummarsa ta bayar wajen ci gaban dan Adam.

c. Sanar da shi yadda zai fuskanci matsalolin da suka addabi al’ummarsa, da kuma sanya masa cewa yana da karfin da zai iya kawo karshensu.

d. Yi masa bayanin dalilan da suka sanya al’ummarsa samun ci baya, da dulmiya cikin jahilci, da mummunan halin da ta fada ciki, da kuma nuna masa cewa zai iya kauce wa wannan, kuma zai iya maganinsa.

e. Yi masa bayanin yiwuwar gyara da za a iya samarwa ta hanyar amfani da karfin da al’ummarsa take da shi.



back 1 2 3 4 5 next