Tattaunawa Ta Goma



Sai na ce maka: Ire-irenka sun dade suna karyar su tsofaffin 'yan Shi'a ne domin su kawo rudu, kuma suna kiran kansu manyan 'yan Shi'a wasu kuwa kanana alhalin a Shi'a babu manya da kanana, wannan yana nuna cewa kai makaryaci ne ba ka ma san Shi'a'nci ba, kana kawo wannan ne domin ka sanya rudu tsakanin Sunna da Shi'a, kuma kai ba Shi'a ba kuma ba Sunna ba.

Sannan dan Shi'a ba ya mamakin falalar Imam Ali (a.s), wannan ya nuna karyar cewa ba ka taba zama dan Shi'a ba.

Saninka da bayin Allah da suke Shi'a ba ya nufin ka yi alfahari, domin ko Annabi don ya sanka ko ka san shi ba abin alfahari ba ne matukar ba ka yi aiki mai imani nagari ba, kamar yadda ayar "yamunnuna…" ta nuna.

Sannan zama da muminai matukar ba ka yi aiki na gari ba shi ma ba abin alfahari ba ne, domin wanda ya zauna hatta da Annabi (s.a.w) amma bai kyautata imani ba duk wuta za shi.

Sannan ka yi karyar sanin sirrin Shi'a alhalin ba ka ma san mene ne Shi'anci ba.

Ka yi karyar sanin ajandar Shi'a, to gaya mana ajendar su a ranar jumma'a mai zuwa, tun da ka yi da'awar sani. Wannan yana nuna bakin jahilcinka, domin ba wanda ya san abin da zai faru gobe. Sannan idan kana nufin ajenda wani tsari da suka shirya to ka sani Shi'a sun fi kowa kishin kasashensu da al'ummarsu, kuma tarihi ya nuna mana yadda suka kare al'ummunsu da dukkan abin da suka mallaka.

Fadinka kai ba sa'ar yaro ba ne, wannan ma yana nufin jahilcinka, sannan ka sani addini ba hauka da karfin tuwo ba ne, addini da ilimi da hankali ne, don haka idan yaro ya fi ka ilimi sai ka rusuna masa.

Koda yake ka yi gadon abin da aka gaya wa Imam Ali (a.s) "Ha'ula'i mash'yakhatu kaumik…"! don haka babu mamaki idan irin wannan kalma ta fito daga bakinka.

Sannan da ka kira malam zakzaki ((tun bai san hukuncin kana wa ak'watuha ba)) wannan ma yabo ne ka yi masa, domin ka nuna da can bai sani ba, amma yanzu ke nan ya sani, don haka wannan yabo ne gareshi da yake nuna cewa yana kara samun ilimi bai tsaya yadda yake dacan ba ke nan.

Amma wanda zai yi maka raddi wallahi ya san wanda yake yi wa raddi, domin yana yi wa wani tantirin jahili raddi ne!!!

Ina ganin ka nuna ba ka neman gaskiya yayin da aka ba ka amsa a bayanin da ka aiko na farko, wanda aka ba ka amsoshi gamsassu:

Ka nuna jahilcinka da siyasar duniya tun farko yayin da ka jahilci gabas ta tsakiya da dukkan abin da yake faruwa tun daga Iran, Iraki, da Labanon, da yadda a yau Isra'ila da Amurka suka kasa, sai suka sanya ire-irenku ku yi ta hanyar alkalumanku, kasashe kuwa irin su Misira sai aka sanya su neman hujumi kan Hizbullah, aka raba ayyuka kowa aka ba shi nasa, don haka mun gane irinku hannayensu.

Sannan nasiha ka daina magana da yawun sunnanci domin sai wasu su dauka sauran musulmi ma'abota mazhabobi kake nufi, ka fadi sunan mazhabinka da tafarkinka da yake kafirta sauran musulmi, idan kuwa babu shi to mun san inda zamu ajiye ka!!!

Hafiz Muhammad Sa'id

May, 1, 2009

 



back 1 2 3