Tattaunawa Ta Goma



Irinka dole ne ya yi musu karamomin kofar ilimomin Annabi (a.s) wanda aka ba shi ilimin kowane abu, tayar da matacce karamin abu ne gun Imam Ali (a.s) akwai abubuwan da suka fi tayar da mamaci mamaki amma ire-irenka da ba su san wilaya da imama da matsayinta a wurin Allah ba dole su musa. Amma da an ruwaito fadin Umar "ya sariyatal jabala" a nan gaskiya ne tun da shi ba ya cikin Ahlul Baiti (a.s)! Amma falalar aali Muhammad (a.s) kowace iri karama da babba kun yi musun ta.

Fadinka kuwa kana cewa: ((Shi kuma Muhd Assaudi a littafinsa Asrarul Fadimiyyah shafi na 98 yace "da badan Aliyu ba da ba'a halicci Annabi Muhd ba kuma da badan Fatima ba da du su biyun ba'a haliccesu ba" shima mawallafin littafin Fatimatuz – Zahra Minal Mahadi Ilal Lahadi bayan ya cika littafin da tatsuniya sai ya ce a shafi na 38 "Tabbas Fatima tana Magana da mahaifiyarta tun tana cikin mahaifa…)).

A nan ma sai na ce: (Ka canja sunan Mas'udi zuwa sa'udi domin ka batar da kama ga mai binciken littafin wannan ma cin amanar ilimi ce)

Ya kai Adam ire-irenka ba zasu iya fahimtar sirrin maganganun Ahlul Baiti (a.s) ba, domin akwai shamaki da Allah ya sanya maka da ba zaka iya fahimta ba. Misalinka kamar misalin "waja'alna fikulubihim akinnatan an yafkahuhu" ne.

Tambaya: me zaka ce game da abin da ya zo a littafin sunan Ibn Majah da sauran sunan cewa ya inganta kuma haka ma gun Shi'a ya inganta cewa; manzon Allah (s.a.w) ya ce: Husain daga gareni yake ni ma daga Husain nake". Ø·­Ø·Â³Ø¸Ù¹Ø¸â€  ظ…ظ†ظ‰ ظˆ ط£ظ†ط§ ظ…ظ† Ø·­Ø·Â³Ø¸Ù¹Ø¸â€ .

Yaya kake ganin wannan, shin kana ganin manzon Allah yana nufin shi ma dan Husain ne?

Ka koma ka bincika, ina ganin bai kamata ba in tsaya bata lokaci wurin yin bayanin da ba zaka iya fahimtarsa ba.

Don haka waccen maganar ma ire-irenka ba sa iya gane ta, saboda "am ala kulubin akfaluha".

Da ka ce: ((Zan tsaya anan sai a a rubutu na na uku.zai zo kuma bayan naga raddin da za'a yi mini ina kira ga kananan yan shi'ar dandalinnnan cewa ni Adamun garin baraya su sani, tsohon dan Shi'a ne sama da shekara 20 da suka wuce du mai musu ko yana neman labari na ya tambayi Mal. Adamu Tsoho Jos ko mal Abubakar Maina ko mal Muttari Sahabi zasu gaya masa waye Adamu. Nasan sirrin Shi'a a fili da boye an kulle kofa dani an tura mu mun kai hari kuma du agendar Shi'ar Najeriya tana a tafin hannuna niba sa'an yaro bane na zauna gaban Zakzaky nayi hidima ya sanni tun bai san hukuncin kana wa ak'watuha ba na sani, to du wanda zai yi mini raddi yasan wa yake yiwa raddi.

Adamu m Adamu, Garin Barayar jahar gombe, A yanzu ina zaune a Kano ne domin kamala karatuna)).



back 1 2 3 next