Tattaunawa Ta Goma



 ((idan kayi baya kadan a shafi na8 wannan malami na addinin Shi'a yace `Allah zai shigar da wanda ya yiwa Aliyu biyayyah Aljanna koda kuwa ya sabawa Allah wanda kuwa ya sabawa Aliyu za'a shigar da shi wuta ko da ya yiwa Allah biyayyah)).

Sai na ce maka: Wadannan maganganu naka suna dada mini haske kan karancin saninka, ka sani hadisai sun inganta daga Sunna da Shi'a cewa; da mutum zai bauta wa Allah shekara saba'in a gefen ka'aba sannan sai ya zo wa Allah yana kin Ali (a.s) da wuta zai tafi. Wannan yana akkasuwa da cewa; idan da ya bi Ali (a.s) babu ma'anar ya saba wa Allah ke nan, ba ana nufin idan ya bi Ali (a.s) amma kuma ya saba wa Allah ba!. Ina ganin kana bukatar koma wa aji idan dai ka taba zuwa, domin irin wannan rashin ganewa naka ya yawaita Adamu.

Ka sani duk wanda ya mutu bai san imaminsa ba kuma bai yi bai'a (imani) da shi ba, to ya yi mutuwar jahiliyya.

Tambaya gaya mana imaminka a wannan zamani!?

Sannan akwai dalilai sai ka koma wa littattafai masu yawa: kamar dalilan da suka kawo cewa da bawa zai bauta wa Allah shekaru dubu tsakanin Rukun da Makam sannan sai ya hadu da Allah yana mai kin Ali (a.s) da Allah ya kifar da shi a cikin wuta ranar kiyama a kan fuskarsa. Manaki na Khawarizimi: 43, 44. A'alamuddin fi sifatil muminin, Dailami: shafi; 400. Ikabul a'amal: 1/242.

Akwai littattafai masu yawa kan wannan lamari sai dai mun takaita a nan saboda gudun tsawaitawa.

Amma da ka ce: ((shi kuwa bakin kafirinnan Ibn Babawaishi cewa yayi a littafinsa Ilalul Shara'iu shafi na 205 "Aliyu dan Abi Dalib zai riga Annabi Muhd SAW shiga Aljannah tabbas)).

Sai na ce maka: Nan ma ka ci amanar nakaltowa ka yi kage ga mabiya Ahlul Baiti (a.s), domin babu wannan managa a wannan shafin.

Sannan da ka ce: ((hakan Hassan dan Abdulwahab ya ce a littafinsa Uyunul Mu'ujuzatu "Hakika Aliyu dan abi Dalibi yana raya matattu kuma yana yaye kuncin masu kunci)).

Sai na ce maka: (Ka canja sunan Husain zuwa Hassan domin ka batar da kama ga mai binciken littafin wannan ma cin amanar ilimi ce)



1 2 3 next