Tattaunawa Ta Bakwai



Sannan kada ka manta lokacin da aka yi mata wannan babu laifi ga Imam Ali (a.s) domin an sanya masa igiya a wuya an ja shi kamar sa, kuma Sayyida Zahara (a.s) ta yi kuka a kofar gida kuma ta yi tawaye da sharadin janyewa idan aka sako shi!!

Ina tsawaitawa saboda na san ba ta da aibi: ina mai cewa; Imam Ali (a.s) ya san za a yi galaba kan sahabbansa da ahlin gidansa bayansa don haka ne ya yi tausasawa sabanin Imam Mahadi (a.s) wanda shi zai tsananta saboda ya san ba za a yi galaba kan mutanensa ba a bayansa.

Imam Ali ya yi kokarin dawo da mutane kan sunnar Annabi (a.s) amma ba su yarda ba, kana iya ganin misali daya daga daruruwan misalai ya yin da ya so ya hana sallar asham sai mabiyansa mayaka suka yi ca da ihu suna wayyo zai kashe sunnar Umar!!!

Kai ba ma shi ba, hatta da Manzo ya yi aiki da irin wannan domin gudun kada irin wadannan lamurra na daukar fansa su biyo baya kan alayensa al'amarin da duk da haka sai da aka yi irin wannan takurawa kansu da tarihi ya kawo!

Ka sani cewa da Imam Ali (a.s) ya dawo da Fadak to a lokacin mai ita ta rasu, sannan da ya dawo da ita ga 'ya'yanta da an sake kwacewa.

 Kai manzon Allah ya dawo da mukamu Ibrahim daga inda jahiliyya suka canja masa wuri ya mayar da shi wurin da Annabi Ibrahim (a.s) ya sanya shi da umarnin Allah amma a lokacin halifa na biyu Umar dan Khaddabi sai ya dawo da shi inda jahiliyya suka ajiye shi. An yi wa Ali (a.s) magana ya sake ajiye shi wurin da Annabi (s.a.w) ya sanya shi amma ya ce yana gudun kada a dauki Ka'aba wasa. Wallahi! da ya ajiye shi inda Annabi (s.a.w) ya sanya shi da bayan wafatinsa a rannan zaka ga ya sake dawowa inda jahiliyya suka mayar da shi.

Don haka wasu abubuwan da ka ga ba su yi ba akwai hikima a ciki; me zaka ce game da manzon Allah (s.a.w) da ya ki yakar kafirai a Makka amma ya yake su a Madina duk da kuwa yana da jarumtakar da ta fi ta Imam Ali (a.s)?!.

Amma abin takaici da kake kawo batun an kashe Imam Husain kana mai nuna cewa: Ai Shi'a ne suka kashe musu malami don haka suka kashe jikokin Annabi (s.a.w). Wane malami ne mutanen da kake cewa rafilawa suka kashe wanda su kuma makiyansu suka kashe jikokin manzon Allah domin su huce haushinsu?!.

Idan kana nufin Shi'a su ne rafilawa ka ba su sunan da ba nasu ba, (koda yake wasu ruwayoyi sun nuna cewa "Saharatu Fir'aun" da suka ki lamarinsa sai ya kira su da wannan suna) Idan kuma wasu sun kashe Imam Husain (a.s) ko sun yi murnar kashe shi domin jin haushin masoyansa to wannan yana nuna batansu da tabewarsu duniya da lahira.

Ka tambayi duniya ka ji waye ya saba kashe mutane za a ba ka amsa da dai a tarihin Shi'a duniya ta san su da juriya da zaluntarsu da ake yi da su da jagororinsu Ahlul Baiti (a.s) har zuwa wannan rana tamu, abin da yake faruwa na zalunci kan Shi'a musamman a Iraki tare da cewa su ne suka fi yawa ya ishe ka misali!.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next