Tattaunawa Ta Bakwai



Da fatan zaka bar ni haka nan domin ba ni da lokacin wadannan bahasosi sosai musamman a wadannan lokuta, wadannan bahasoshi ne da suka gajiyar da musulmi, ina ganin lokaci ya yi da kowa zai kiyaye kimar abin da kowa yake a kai ba tare da ya yi suka ko isgili da abin da wani yake girmamawa ba, kai komai kimar mutum yanzu a wurina idan ya yi suka ga wani ra'ayi ko isgili to da ni da shi mun raba gida, don haka ina ganin ka dage da bincike idan ka kai ga natija kowace iri ce har a zuciyarka to ka yi tsarkin niyya a kanta ka bi ta, amma ka kuma shirya wa amsar da zaka ba wa Ubangijinka a ranar lahira bias abin da ka gamsu a kansa. Allah ya sa mu dace.

Game da amsarka ta ba dole ba ne saninka, sai in ce: Babu damuwa, duk inda muke abin nema ita ce yardar Allah, amma ganin kamar ka damu da wadannan bahasosi ne, wadanda suke nuna kyakkyawar niyyarka ta neman sanin makomarka da kuma ikhlasinka na ganin an yi addini da hujja kamar yadda yake tun farko daga ma'aikin Allah ne ya sanya na ga bari in hada ka da wani domin ku yi ta yin bahasi, amma idan ba haka ba ban taba tambayarka wannan ba.

Kada ka damu da ganin mutane sun bace ko sun kauce wa hanya wannan abu ne wanda na zauna cikinsa ni ma kusan shekaru sama da goma amma daga baya na cimma natijar cewa; idan duk duniya zasu koma kafirci to bai kamata mutum ya damu kansa ba kuma wannan ne umarnin Allah ga annabinsa, sai dai kowa ya tsaya gun haddin nasa kada ya taba na wani, wannan shi ne kawai zai sanya kowa ya koma bincike da kuma samun zaman lafiya tsakanin al'Ummu gaba daya, kuma wannan ne musulunci ya zo da shi daga wanda ya fi kowa kishinmu fiye da kawukanmu. Kada ka manta cewa; ba yadda za a yi mutane su koma yadda kake so, domin Allah ma bai yi su domin ya gan su yadda yake so ba, sai dai shi zai kama kowa da kaucewarsa ne bayan ya dora musu hujja da aiko manzanni da isar da sako.

Amma dagewarka a kan sai ka ci gaba da wannan bahasin ina ganin ba ka son ka bar wannan bahasi, ka sani ya kamata ne kowa ya riki abin da ya yi yakini da shi ba tare da samun damuwa da na wani ba, sannan duk wanda ka gamsu da shi daidai hakan ne Allah zai yi maka hisabi. Sannan ni a wannan kwanakin ina da karancin lokaci matuka da gaske don yin wadannan bahasosi, don haka ne ma nakan dan jima wani lokaci ban koma wa email ba.

Amma ayoyin da kake kawo wa domin nuna ismar sahabbai da cewa ba sa sabo ko kuma dole dukkaninsu daya ne makomarsu daya, Ayoyi ne da ka kawo masu nuna cewa akwai itlaki a cikinsu, don haka Allah madaukaki mai hikima ya kawo musu kaidoji kamar: "waman nakasa fa'innama yankusu ala nafsih" da "wamimman haulakun minal a'arabi…" da "izaja'akal munafikuna…" da "…in kalabatum ala a'akabikum, faman yankalib…" da "faman nakasa fa'innama yankusu ala nafsihi…" da "…wa'adallahul lazina amanu minhum…". Hatta da irinsu "hazani hashamani…" a karshenta akwai kaidi da cewa; "fallazina kafaru kutti'ata lahum siyabum minannar…".

Sannan da kake ayyana wadanda ake nufi ina ganin zai zama shisshigi idan muka ayyana wadanda ake nufi ba tare da wani haske daga Littafin Allah ko hadisi sahihi ba. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa da halifa na farko (kamar yadda ya zo a littafin muwatta'I Malik), bayan ya tambaye shi ya ki sheda masa da alheri a duniya ya tambayi Annabi (s.a.w) dalili. Annabi (s.a.w) ya amsa masa da cewa domin ban san abin da zaku yi bayana ba! Amma sai ga shi kana nuna wa Allah su wa yake nufi da wadannan ayoyi kana mai kawo sunaye. Ayoyin Kur'ani mai daraja mutlakai ba ka iya ayyana masadik dinsu a ka'ida sai ka dogara da shari'a. Kamar yadda manzon rahama da kansa ya nuna su waye; Ahlul Baiti (a.s) kuma ya nuna su waye nisa'ana, kuma ya nuna waye wallazina amanul lazina yukimunassalata…, da sauran wurare.

Ina ganin lokaci ya yi da zaka guji yin tafsiri da ra'ayi da ka so domin ya yi daidai da mazhabarka, ka nemi taimako daga hasken ruwayoyi sahihai, ka koma wa littafi da hadisai ingantattu tukun.

Na ji dadi da na ga ka yi nuni da wannan ka'ida da na lurasshe ka "wa'inna au iyyakum la'ala hudan…" ina fatan ka lizimce ta, sai dai ka yi amfani da ita a mahallinta.

Sannan da kake cewa; Kana ganin Allah zai yarda da mutum kuma yayi kuskure a sha'anin da Allah ya yadda da shi akai kana mai kawo ayoyi kamar haka: (wallazinattaba'uhum bi ihsanin radiyallahu anhum wa radu anhu) (Allazina in makkannahum fil ardi akamussalata wa atawuzzakata wa amaru bil ma'arufi wa nahau anil munkar...) da sauransu, sannan kuma daga karshen maganarka kana musun wilayar Ali (a.s), kana mai  da'awar abin da babu shi; a yaushe ne malamai suka yi musun wilayar Imam Ali (a.s) a yaushe ne suka ce hadisan maudu'ai ne, a yaushe ne wannan ya faru alhalin Buhari da Muslim da ibn majah da Tirmiji da Ahmad da Hakim da sauran manyan maruwaita suna karfafa wilayar Imam Ali (a.s) kai ga ma sauran mafassara Kur'ani. Ga Umar dan Khaddabi yana furuci da wannan fifiko na Imam Ali (a.s) amma waye ya isa ya yi musun wannan daraja da daukak bayan Umar ya tabbatar da ita gareshi!

Ga shi a ranar Gadir Umar yana cewa da shi: Farin ciki ya tabbata gareka ya dan Abi Dalib, hakika ka wayi gari kana shugabana kuma shugaban dukkan mumini da mumina. Ga wasu daga cikin wadannan masdarori da suka yi bayani game da Gadir karara da bayanai dalla-dalla da shelanta wilayar imam Ali da babu mai musu sai munafuki, da kuma murnar da Umar dan Khaddabi ya taya shi kamar haka:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next