Tattaunawa Ta Biyar



Ina ganin ba ka san me kake cewa ba, ka nemi taimakon malamanka ka dakatar da magana, ka sani tanakudinka da warwarar maganarka sun yawaita, ka ce: kaburbura zuwa wajensu bauta ne, kuma ka ce an yarda mu je yanzu, ke nan Allah (S.W.T) da manzonsa (s.a.w) sun yi umarni da bautar kaburbura ke nan! Wal’iyazu billah!.

Amma maganar da kake yi na cewa Fikihu zai iya saba wa ma'aiki kuma ya yi daidai, kana mai nuni da cewa; shi kansa (s.a.w) ya sha ruwa kuma ya ce asha ruwa a lokacin. Sai na ce maka: Tir da fikihun da ya saba wa maganar Annabi, Allah ya tsare mu da shi, kuma wannan fikihun ba musulunci ba ne koda ka kira shi da hakan, kuma ka sani dukkan aikin Annabi (s.a.w) musulunci ne, babu wani abu da Annabi (s.a.w) yake yi da ya fita daga da’irar musulunci.

Sannan kuma shan ruwa idan kana nufin na azumi ne to akwai dalili da ya zo daga Kur’ani mai girma da sunnar Annabi (s.a.w) da zai sanya ka shan ruwa, idan kuma wani abu kake nufi daban to sai ka fada.

Sannan a ina ka samu hujjar maganarka ta cewa duk abin da yake wajen sahihain ba dole ba ne ya zama hujja. Ka sani Buhari da Muslim sun tara hadisai ne masu yawa kuma amma sun takaita da dan kadan daga abin da suka tattara, da wace hujja ne suka san sauran ba daidai ba ne?. ko kuma Allah da Manzo (s.a.w) ne suka yi bayani game da cewa Buhari da Muslim su kadai ne hujja!

Kamar yadda muka fada baya ne: Tara hadisai an fara shi ne; bayan kowa yana da nasa bangare, don haka kowa yana da nasa abin da yake karewa.

Ka rika sanin abin da kake cewa: Ka sani hujja tana cikin biyayya ga Littafin Allah da wasiyyan Annabi (s.a.w) wannan kuma su ne hujja a kan kowa, idan wani ya ki bin su wannan shi ya jiwo wa kansa, wannan kuwa ko musulmin tun lokacin Manzo (s.a.w) ko a yau ko a nan gaba, kamar yadda sauran kafiran duniya duk wannan hujja ne kansu.

Na ga ka kawo wasu ayoyin Kur’ani madaukaki kana maganarsu ba a mahallinsu ba, kuma ka kawo wani hadisi da Manzo (s.a.w) ya gargadi wani sahabi da ya zagi wani sahabin, kamar yadda ya zo cewa Khalid ya zagi Abdurrahman sai Manzo (s.a.w) ya yi masa gargadi: Ban sani ba me kake so ka ce game da su.

Sannan kuma me zaka ce game da la’antar Imam Ali (a.s) shekara tamanin da Mu'awiya ya assasa, kai kana ma iya zuwa farko yayin da Umar bn Khaddabi yake cewa da Abu huraira: Amima Ko Umaima ba ta yo kashinka ba domin ka zama jagoran mutane. Shin kana ganin sahabi ya zagi sahabi ne ko me kake gani, sannan kuma me ye fa’idar tayar da wannan bahasi?! Ina ganin ka rude matuka! Ba ka san me kake son cewa ba, sannan ba ka san me zaka gaya wa waninka ba.

Sannan kuma idan kana ganin hujja a wajenka ba ta da wani matsayi ko kima to sai ka yi addininka da yadda kake gani, domin kai ne abin tambaya kan ayyukanka ba ni ba, kuma a lahira ba ka da wata hujja a kaina kamar yadda kake neman nunawa. Wannan ya rage naka ne ka cigaba da bincike ko ka bari.

Kuma daga karshe ina son yi maka nasiha kan cewa ka daina zargi da cewa; za a zagi kowane irin mutum ne balle ka yi zargin zagin wasiyyan Annabi (a.s) ko annabin (s.a.w) ma kansa, idan ba ka da hujja sai ka yi shiru, domin zargi mummuna ba ya nuna komai sai hali maras kyau.

A natijar wannan bahasin mun cin ma abubuwa kamar haka: Na daya: Ahlul bait (a.s) su ne kadai makoma da Allah (S.W.T) da manzonsa (s.a.w) suka bari tare da Kur’ani mai daraja. Na biyu: Maganar manzon Allah (s.a.w) ita ce hujja, kuma ya yi wasiyya da Ahlul Bait (a.s). Na uku: Ahlul Baiti (a.s) su goma sha biyu ne, kuma Shi'a imamiyya suna biyayya garesu gaba daya a matsayinsu na halifofin Annabi (s.a.w) da Allah ya ayyana masa. Na hudu: Tun farkon zuwan Manzo (s.a.w) ya ambaci kalmar halifa da waziri ga Imam Ali (a.s). Na biyar: Har yanzu ka kasa nuna waye jagoranka da kake biyayya gareshi, ko kuma ma ba ka san shi ba!

Hafiz Muhammad

Kammala gyarawa

01 /July/ 2009

 



back 1 2 3 4 5 6