Tattaunawa Ta Biyar



Wannan kadan ke nan daga wuraren da manzon Allah (s.a.w) ya yi amfani da kalmar wazirinsa ga Imam Ali (a.s). Hada da abin da ka sani wanda ka kawo na yakin Tabuka, wanda shi ne na takwas a lissafinmu. Akwai hadisin a musnad Ahmad ya ce: wannan hadisi isnadinsa ingantacce ne. musnad, 1: 545.

Ka sani Manzo ya shelanta matsayin Imam Ali (a.s) a wurare da yawa da malaman Sunna suka ruwaito, duba ka ga me nisa’i ya kawo a khasa’is dinsa: 49-50. da yake cewa: manzon Allah (s.a.w) ya ce; kai ne halifana bayana kan kowane mumini da mumina, kai matsayinka gareni kamar na haruna ga musa, kai ne halifata a kan kowane mumini bayana.

Hada da abin da abu ya’ala a Masnad dinsa da kuma Mustadrak: 3: 1333. da tarihi damishk: 1: 209. da tarihi ibn kasir : m 4, j 7: 338. da isaba na ibn Hajar: 4; 270. da sauransu. duk sun kawo cewa: manzon rahama (s.a.w) ya ce: ba zai yiwu ba in tafi sai kana halifana.

Amma game da auren mutu'a da ka kawo ka sani ya inganta daga Imam Sadik (a.s) cewa: Mutu'a addinisa ce, kuma addinin kakanninsa ba. Sai dai ina nufin kana nufin ya ce: "Takiyya addinisa ce, kuma addinin kakannina", kuma haka ne wannan ya inganta daga Imam Sadik (a.s). Amma batun da ka kawo na cewa; Annabi (s.a.w) ya haramta Mutu'a a yakin Khaibar wannan labari ne da aka jingina shi ga Imam Ali (a.s) don a rusa tafarkinsa, kuma wannan bai inganta ba, domin ya ci karo da Kur’ani kuma ya ci karo da abin da ya zo mutawatiri daga Imam Sadik (a.s), daga kakansa Imam Ali (a.s), kuma tun da hadisin aahad ne, to bai isa ya rusa Kur'ani ko mutawatirin hadisi ba.

Sannan duba tarihin halifofi na Suyudi ka gani a babin awwaliyati Umar, cewa shi ne farkon wanda ya haramta auren mutu’a. Maliku ya kawo shi a muwatta’ Umar ya hana kuma ya kira shi da nikahussirri.

Ka kuma duba fadin Umar bn Khaddab cewa: Mutu’a biyu ta kasance a lokacin manzon Allah (s.a.w) amma ni na haramta su kuma ina ukuba a kai: Auren mutu’a da hajjin tamattu’i. Littattafai da dama sun kawo kamar Mugni na ibn kuddama bahambale.

Bayanin cewa Umar shi ne ya haramta auren mutu’a kan al’amarin ibn haris ya shahara sosai tsakanin malaman Sunna da Shi'a koda kuwa wasu masu kawo rudu a wannan zamani sun so hakan.

Allah waddan naka ya lalace; kai tir da masu musun hadisi ingantacce kamar fadin manzon Allah (s.a.w) game da kasancewar Imam Ali birnin ilminsa: Ban san sa’adda ka zama Harrani ba da zaka rika dukan falalar Imam Ali (a.s) ba tare da wani dalili ba, kai ba dan yankin HARRAN ba ne, balle ka taso da kin Ahlul Bait (a.s), ban sani ba ko gaba da wannan gida ya zo mana Nijeriya ne daga koyarwarsa, sai ya zama duk wani abu ingantacce daga Ahlul Bait (a.s) musamman game da Imam Ali (a.s) sai a rika gaba da shi.

Hadisin kasancewar Imam Ali (a.s) kofar birnin ilimin Annabi (s.a.w) yana daga musallamat gun dukkan musulmi har sai da Dan Harran ya zo yana inkarin duk wata falala ta Imam Ali (a.s), wannan kuwa ba mamaki domin shi dan HARRAN ne wanda yanki ne da suka sha gaba da wannan gida tun lokacin Mu'awiya dan Abu Sufyan.

Alharrani ya karyata wannan hadisi kuma ya danganta wadanda suka ruwaito shi da cewa zindikai, alhalin daga cikin masu ruwayar wannan hadisi akwai: Imam Ali (a.s) kansa, da Hasan da Husain â€کya’yansa, da Abdullahi dan Abbas, da Jabir dan Abdullah, da Abdullahi dan Mas'ud, da Huzaifa alyamani, da Abdullahi bn Umar, da anas dan Malik, da amru dan asi, daga tabi’ai akwai Yahaya bn mu’in, da Ahmad dan Hambal, da Tirmizi, da Bazzar, da Dabari, da Hakim, da Baihaki, da ibn Asir, da da nawawi, da ala’ai, da ibn Hajar Askalani, da sakhawi, da Suyudi, da Makki, da sauransu, kuma abin mamaki ga Harrani da dukda ya dogara kan Yahaya bn mu’in da Tirmizi da Hakim a wajan karbar hadisansu, amma sai ga shi sun ruwaito hadisai da dama game da Imam Ali (a.s) amma ya ki karbar wannan daga garesu. Tirmizi ya karfafi wannan hadisi da cewa kyakkyawa ne, amma wajen â€کya’yan HARRAN da wutar gaba da Alayen Annabi (a.s) ta huru a cikinsu a irin wadannan wurare makauniyar gaba ta rufe musu ido!.



back 1 2 3 4 5 6 next