Tattaunawa Ta Biyar



Ammam da kake cewa kalmar "Wali" ba a fili take ba, kuma ka yi da'awar yardar Allah ga duk wanda ya yi halifanci kafin Ali (a.s), sai in ce maka: Yana da kyau ka yi wa kanka adalci: ina ganin ka kasa fahimtar abin da na kawo don haka ka koma sosai ka duba, ka kuma nemi taimakon malamanka a kai, kan batun "amm" da "khas" da na kawo. Sannan kuma wani abin mamaki shi ne dukkan hadisai da karinonin da na kawo sai ga shi kana maganar karina a kai. Ka koma wa bayanin baya zaka ga karinonin da na kawo na wasu ayoyi da hadisai da suka karfafi wannan maganar, hada da cewa farkon hudubar Manzo (s.a.w) da karshenta duk yana nuna wannan karinar karara. Wadannan karinonin kuwa a cikinsu akwai: “zikra liman kana lahu kalbun au alkas’sam’a wahuwa shaheedâ€‌.

Amma batun da kake cewa ba a ruwaito hadisin Gadir ba sai in ce maka: Sahabban da suka rawaito Gadir suna da yawa kwarai matuka, ka koma wa littafin Gadir na Allama Sheikh Amini ka sha mamaki, kuma akwai ruwayoyi sama da 360 da ya yi nuni da su, wadanda sun zo game da Gadir daga sama da sahabi 125.

Sannan kada ka dauka in ka kaddara masu ruwaya koda daya ce idan ta inganta ba ta zama hujja, domin ku kun doru a abubuwa da yawa kan ruwaya guda ne hatta a al’amarin akida. Wannan hadisin an kasa boye shi, don haka ya zo hannun mutane da ikon Allah (S.W.T), amma akwai wasu hadisai da siyasa ta kan sanya a ki yada su, ko kuma boye wasu kalmominsu ko canza su kamar karshen hadisin halifofin Annabi (s.a.w).

Amma da'awar cewa Annabi (s.a.w) ya yi mummunar addu'a ga wanda ya ki biyayya ga Ali (a.s) da cewa wannan ya saba wa usulubin da'awa ta gari da da'awarka ta cewa Annabi (s.a.w) ba ya yi wa al'umma addu'a mummuna da fakewa da cewa rashin taimakawar yana iya kasancewa cikin rashin sani. Sai na ce maka: Duk wannan babu kokwanto cikin shari’a idan ta inganta, amma a cikin maganganunka akwai alamar tsananin kushewa game da abin da ya zo yana yabon Ahlul Bait (a.s). ko kuma yana ba su wata falala, wannan ba ya cikin dabi’ar mumini. Kada tafarkinka ya kai ka cikin tabewa! Sannan abin da ka fada na cewa ya saba wa da’awar Annabi (s.a.w) da Kur’ani mai girma ta la’antar duk wani wanda ya saba wa tafarki bayan gaskiya ta zo masa: surar “Tabbata yada Abi lahabinâ€‌ babban misali ne gareka. Hada da abin da yazo yana la’antar magabata kamar su Fir’auna da wadanda suka gabace shi da wadanda suka zo bayansa. Hada da la’antar munafikai da Kur’ani ya yi, da masu cutar da Annabi (s.a.w) aka kuma muzanta su muzantawa mai muni kamar kiransu marasa hankali da sauransu.

Amma da'awar ayar tablig a Arfa da ka yi hakika masdarori sun zo suna masu tabbatar da saukar wannan aya a Gadir, akwai dalilai masu yawa kan hakan, sannan kuma wasu sun kawo ta game da cewa a ranar hajjin wada’ ne. wasu kuma sun hada duka biyun ne, kuma wannan me sauki ne, ana iya hada su.

Sannan musun hadisi ko ingancinsa saboda ya yabi ahlul baita (a.s) wani abu ne da na fahimta yayin da kake maganar musun ruwayar Suyudi, ka sani wannan ya inganta daga littattafai masu yawa: tun kafin Suyudi, amma wani abin da nake fahimta daga wajenka duk wata magana da ta yabi Imam Ali (a.s) ko Ahlul Bait (a.s) ko ta karfafi wilayarsu, to kana kokwanton ingancinta ba tare da ilimi ba, ko kuma saboda inadi ne! Shiblanji ya karbo shi daga sa’alabi, sannan kuma halbi ya kawo shi mursali a matsayin wani hadisi da aka sallama wa ingancinsa, a siratul halbiyya, j 3, shafi 214.

Amma batun me Annabi (s.a.w) ya bari: wannan maganar ta abin da Annabi (s.a.w) ya bari wanda ya mutu a kai ya gabata, kuma ya riga ya tabbata cewa; shi ne tafarkin da Ahlul Bait (a.s) suke kai, su ne ma’auni da za a koma gareshi yayin sabani. Addini ya cika, kuma daga cikin cikarsa akwai biyayya ga Ahlul Bait (a.s) kamar yadda Manzo (s.a.w) ya yi wasiyya da bin su, wannan duk yana daga cikar addini. Allah (S.W.T) da manzonsa (s.a.w) sun barranta daga wautar da ake jingina musu, Manzo (s.a.w) ya san wannan addini shi ne karshe, kuma yana da hadafin shiryar da mutane gaba daya, ba zai yiwu ba ya tafi ya bar su kara zube, ba su san inda zasu dafa ba.

Kuma wannan rashin hikima abin takaici ba wanda ake jingina wa shi sai mafi hikimar bayin Ubangiji, kowane jagora zai tafi yana nuna wa al’umma makomar da ya kamata ta bi, amma sai Annabi (s.a.w) ne ake jingina wa rashin hadafi!

Amma batun da'awar da ka yi na cewa Allah (s.w.t) ya yi alkawarin kare sunnar ma'aiki sai na ce maka: Allah bai yi alkawarin kare Sunna ba, ya yi alkawarin kare Kur’ani ne! don haka ne ma Sunna take cike da mai inganci da waninsa: Wannan ne ma ya kawo ilimin hadisi da masu ruwayarsa da sauransu. Abin mamaki rashin ma’auni da kuma wata ka’ida ko madogara mai kyau da kake da ita, ya sanya ka kana magana kana warwara. Kana musun wata sunnar ta Annabi (s.a.w) da ya bari saboda ta yabi ko ta shugabantar da Ahlul Bait (a.s). a lokaci guda kuma kana cewa Allah ya yi alkawarin kare ta. Idan ka san Allah ya yi alkawarin kare ta to don me kake wahalar da mutane wajen musun ta da neman ba ka hujjoji kan ingancinta!?

Sannan ka ce ana kokarin jifan wasu da munafunci, wannan kuma wani abu ne da ka fahimta kuma ba na iya shiga kwakwalwarka in hana ka fahimtar abin da ka dama. Amma abu guda shi ne yana da kyau ka nisanci zargi domin ba shi da kyau.



1 2 3 4 5 6 next