Bada'i(Canjawa)



Sai dai wanan jawabi bai isa ba, domin kur’ani wani abu ne da ake fahimtarsa daga dukkan kur’ani, ba daga wani bangare ba kawai. Wannan kusan muna iya cewa yana zama rabin amsa ne, domin akwai wani bangare da yake jingina canji ga Allah da cewa: “Allah yana shafe abin da ya so yana kuma tabbatar da abin da ya so kuma a gunsa akwai Ummul kitab”[5].

Da fadinsa madaukakin sarki: “Allah ba ya canja abin da ke ga mutane har sai sun canja abin da yake ga kawukansu”.

Aya ta farko tana nuna Allah yana shafe abin da ya so yana kuma tababtar da abin da ya so wanda wannan yake nuna canji da sakewa, amma aya ta biyu ta shelanta a fili cewa Allah ba ya canja halin mutane idan suka canja abin da yake ga kawukansu. Al’amarin tattalin arziki da siyasa na mutane yana nufin wani abu ne da Allah yake kaddara shi da zai iya karbar canji idan mutane suka canja rayuwarsu daga shirka zuwa ga imani, daga bata zuwa ga shiriya, to a nan akwai kaddarawa guda biyu; kaddarawa da ta zo daga halin mutane na biyayyarsu, da kuma kaddarawar Allah garesu a halin sabonsu, idan suka zabi biyayya sai a gudanar musu da na farko idan kuma suka zabi sabo sai a gudanar musu da al’amari na biyu, da kana ne abin da ya zo a ruwaya da yake nuna tasirin ayyuka wajan arzutawa da ajali da bala’o’i yake nuni.

Wannan kuma ba wanda ya saba daga muslumi game da hakan; sabani ya samu ne kan ma’anar “Bada” idan aka fassara shi ta yadda zai saba da ma’anar da ya saba da lugga da ya kore tauhidi, amma sabanin zai kau idan aka komawa ma’anar da ake nufi a isdilahi da ba ya lizimtar danganta jahilci ga Allah (S.W.T). Abin da ake nufi a koyarwar Ahlul baiti (A.S) shi ne “Allah yana kaddara wa bayi wani abu sannan sai ya canja sakamakon wani abu sabo da ya bayyana daga bawa sakamakon wani aiki daban da ya yi, tare da cewa Allah ya riga ya san duka al’amuran biyu zasu faru a dukkan halayen biyu”.

Da sun san wannan ma’ana da sun san cewa wannan wani abu ne da dukkan msulmi suka hadu akansa. Shi ya sa jayayya din kan lafazi ne kawai, kuma Allama Sayyid Abdulhusaini Sharafuddin ya yi gaskiya yayin da ya ce: “Jayayya tsakaninmu da Ahlussunna ta lafazi ce. Sannan sai ya ce: Idan waninmu ya dage a kan wanann jayayya ya ki yadda da ma’anar ‘Bada’ kamar yadda muka fada, to mu sai mu sauka a kan hukuncinsa sai ya canja lafazin da abin da ya so, ya kuma ji tsoron Allah a kan dau’uwansa mumini[6].

Kafinsa akwai Shaihul Mufid a littafinsa yana cewa; “Amma amfani da kalmar Bada wannan ruwaya ce ta zo da ita wacce abu ne da yake tsakanin Allah da bayinsa, ba domin ruwaya ta zo da shi ba da take da inganci da bai halatta ba a yi amfani da shi ga Allah (S.W.T), kamar yadda da ba don ruwaya ta zo da cewa Allah yana fushi, yana yarda, yana so, yana jiji-da-kai, da bai halatta a gaya masa haka ba, sai dai yayin da ya zo a ruwaya sai ya zama yana da ma’anar da hankula suka tafi akai da ba sa kin ta, kuma tsakanina da sauran msulmi a wannan babi babu sabani, kawai sabanin da ake dashi a lafazi ne ba a wani abu ba, na kuma riga na yi bayanin dalili na a kan amfani da wannan lafazi. Wannan kuma shi ne mazhabar imamiyya gaba daya, kuma duk wanda ya saba wa wannan mazhaba yana sabani ne a lafazi ba a ma’ana ba[7].

Kafinsa Imam Assadiq (A.S) ya fada a tafsirin ayar nan: “Allah yana shafe abin da ya so yana kuma tabbatar wa kuma a gunsa akwai Ummul kitab”. Ya ce; “Dukkan wani al’amari da Allah yake son shi to akwai shi a cikin iliminsa kafin samar da shi, ba wani abu da yake bayyana gareshi sai ya kasance da ma can yana da ilimi da shi, Allah ba ya canja wa sakamakon jahilici”[8]. A wani hadisin yana cewa: “Wanda ya raya cewa Allah madaukakin sarki yana samun canaji a wani abu, da bai san shi ba jiya, to ka barranta da shi”[9]. Sannan madogarar dalilin imamiyya a mas’alar Bada a bu uku ne:

1-Faidansa: “Allah yana shafe abin da da ya so ya kuma tabbatar da abin da ya so kuma a gunsa akwai Ummul kitab”[10].

Da fadinsa: “Wanda yake sama da kasa yana tambayarsa, kowace rana yana cikin sha’ani ne”[11].

2-Kamantuwar wanann mas’ala da mas’alar shafe hukunci a shari’a, Bada shafewa ne a samarwa, Naskh kuma shafewa ne a hukunci. Kamar yadda msulmi suka tabbatar da shafewa ga hukunci a shari’a kamar a mas’alar alkibla daga masallacin al’akasa zuwa ga masallacin ka’aba, kuma ba wanda ya saba a wannan na daga musulmi. Wannan kuma ba a gan shi a matsayin canji a ilimin Allah ba, bai kuma lizimtawa Allah jahilci ba da ya gabata, haka nan mas’alar Bada canji ne amma a samarwa ba tare da ya lizimta wa Allah jahilci da ya rigaya ba, ko sabawa ga iliminsa na tun fil azal, idan wani ya kawo matsala game da Bada, to sai ya kawo matsala game da shafewa, abin da duk muka fada game da shi a babin shafe hukunci haka ma yana iya zama dalili a babin Bada ba tare da wani bambanci ba ko kadan tsakanin al’amuran biyu. Suka a kan Bada yana zama maimaitawa ne ga sukan da yahudawa suka yi wa shafe hukunci a farkon shari’a yayin da suke ganin wanan bata ne da kuma rashin yiwuwar danganta shi ga Allah (S.W.T) kamar yadda ya zo na daga amsoshi da malaman msulmi suka ba su da kuma tabbatar musu da yiwuwar shafe shari’a ba tare da wanan ya lizimta samuwar tawaya ga zatin Allah madaukakin sarki ba, haka ma wannan yake yiwuwa ga Bada a babin halittawa da samarwa da kuma tafiyar da al’amuran bayi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next