Bada'i(Canjawa)



 Musulunci shi ne addinin Allah dawwamamme da hakikarsa ta bayyana cikin nassin littafin Allah (S.W.T) da sunnar manzonsa (S.A.W) da ba ya magana da son rai sai da wahayi. Kuma Allah da manzonsa sun sani cewa al’ummarsa zata yi sabani bayansa kamar yadda ta yi sabani a lokacin rayuwarsa, don haka ne Kur’ani mai girma ya sanya wa al’umma makoma da zasu dogara da ita bayan wafatin manzo (S.A.W) tana tafiya tare da shi taku-taku tana kuma gabatar wa al’umma abin da suka takaita ga fahimtarsa da tafsirinsa, wannan kuwa su ne; Ahlul Baiti (A.S), sun tsarkaka ne daga dukkan dauda da kuma kazanta wadanda Kur’ani ya sauka ga kakansu Mustapha (S.A.W), suna karbarsa suna karanta shi suna hankaltarsa da kiyayewa, sai Allah ya ba su abin da bai ba waninsu ba... Kamar yadda manzo ya yi wasiyya da su a matsayin makoma ta gaba daya a hadisin sakalain mash’huri, sai suka kwadaitu wajan kare shari’ar musulunci da Kur’ani mai girma daga fahimta ta kuskure da tafsiri na barna, suka saba da bayanin ma’anarsa madaukakiya, sai suka zama makoma kuma madogara ga al’ummar musulmi, suna kore shubuha suna masu karbar tambayoyi da hakuri da juriya. Bayan nan abin da suka bari mai yawa yana shaidawa da kyawon mu’amalarsu tare da masu tambayarsu da tattaunawa da su, kuma komawa garesu da zurfin amsawarsu yana nuni zuwa ga kasancewarsu makoma ta ilimi a wannan fage.

Hakika koyarwarsu ta kare abin da suka bari, kuma mabiyansu suka kwadaitu a kan kare shi daga tozarta, abin da yake nuni zuwa ga koyarwarsu da ta tattaro dukkan wasu rassa na ilimomin da suke kunshe cikin koyarwar addinin musulunci.

Kuma wannan makaranta ta iya tarbiyyatar da mutane da suke shirye domin kamfata daga wannan ilmi kuma ta fitar wa al’umma manyan malamai masu biyayya ga tafarkin Ahlul baiti (A.S), suna masu gamewa da sanin dukkan mas’alolin mazhabobi daban-daban, da kuma akidoji a cikin da’irar musulunci da wajanta, suna masu bayar da mafi kyawon amsa da bayanai a tsawon zamanin da ya gabata.

Hakika majma Ahlul baiti (A.S) ya gaggauta yana mai farawa daga nauyin da yake kansa da ya dauka a kafadunsa domin kariya ga sakon musulunci wanda ma’abota mazhabobi da kuma masu akidu da suka saba wa musulunci suka damfaru da su, yana mai bin tafarkin Ahlul Baiti (A.S) da mabiyansu da suka kwadaitar da raddi kan kalu-balen wannan zamani da kuma kokarin dawwama a kan tafarkin gwagwarmaya daidai gwargwadon abin da kowane zamani yake bukata.

Ilimin da littattafan malamai masana ma’abota bin koyarwar Ahlul baiti (A.S) suka taskace shi a wannan al’amari ba shi da misali, domin shi madogara ce ta ilmi da yake karfafa da dogara da hankali da hujja, yake kuma nisantar son rai da zargi, yake kuma magana da malamai masu tunani daga ma’abota kwarewa, maganar da hankali yake yarda da ita kuma dabi’ar dan Adam kubutacciya take karbar ta.

Kokarin majma ya zo ne domin ganin an gabatar wa dalibai sabuwar marhalar wannan ilimi mai wadata a shafin tattaunawa da tambaya da kuma raddin shubuha da a kan tayar daga lokaci zuwa lokaci tsawon zamani, ko kuma ake kawo wa a yau musamman ma da taimakon wasu kungiyoyi masu kin musulunci da musulmi a cikin sarkar sama ta intanet da makamantansu, muna masu nisantar abin da yake maras kyau, muna masu kwadayin motsa tunanin masu hankali da masu neman gaskiya domin su bude idanunsu a kan gaskiyar da koyarwar da Ahlul baiti (A.S) suka gabatar wa duniya baki daya a zamanin da hankula suke cika, alakar mutane da tunani take samuwa cikin gaggawa.

Ba makawa mu yi nuni da cewa wannan tattararrun bahasosi an tanade su ne a lujna ta musamman da Hujjatul Islam Abul Fadal Islami yake shugabanta tare da wasu manya da suka hada da Sayyid Munzir Hakim, da Shaikh Abudlkarim Bahabahani, da Sayyid Abdurrahim Musawi, da Shaikh Abdul Amir Assuldani, da Shaikh Muhammadul Amini, da Shaikh Muhammad Hashimi Al’amili, da Sayyid Muhammad Rida aali Ayyub, da Shaikh Ali Baharami, da Husaini Salihi, da Aziz Al’ukabi.

Kuma muna mika godiya mai yawa ga dukkan wadanan da kuma ma’abota falala da bincike da suka hada da: Shaikh Yusuf Garawi, da Shaikh Ja’afarul Hadi, da Ustaz Sa’ib Abdulhamid, domin bibiyar da kowannensu ya yi wa wadannan bahasosi da kuma bayanansu masu kima.

Fatanmu shi ne ya zama mun gabatar da abin da zamu iya na kokarin sauke nauyin da yake kanmu game da wannan sako mai girma na ubangijinmu da ya aiko manzonsa da shiriya da kuma addinin gaskiya domin ya daukaka shi a kan dukkan wani addini kuma Allah ya isa shaida.

Majma Ahlul baiti (A.S)
Qom

 

Bada A Cikin Kur’ani Mai Girma

Ana la’akari da ‘Bada’ a cikin al’amura na kalam na tauhidi da aka tayar da bahasi mai fadi akansa tsakanin malaman kalam. wanna kuma ya faru saboda wasu abubuwa masu jan hankali da suke kan maganar Bada ne. Domin Bada a lugga yana nufin bayyana bayan boyuwa. yana kuma hadawa da tattaunawa ta al’ada, da kuma wajan musanya ra’ayoyi da tunani da hadafi da manufofi, misalin a kan ce: “Da ra’ayinsa kaza ne sannan sai ya samu canji a game da ra’ayin” Abu ne sananne cewa canjin ra’ayi da wannan ma’ana tana kunshe da ma’anar jahilci da ya rigaya, da kuma faruwar sabon ilmi kan al’amarin. kuma dukkansu koraru ne ga Allah madaukakin sarki domin ilmin Allah madaukakin sarki ainihin Allah ne, babu wani jahilci da ya rigaye shi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next