Tsarin Siyasa A Musulunci



Mu sani cewa; tafiyar da al’amarin siyasa da jagorancin al’umma abu ne na wadanda Allah ya zaba ya mika musu ya sanya shi a hannunsu wadanda muka ce imma dai annabi (A.S) ko kuma wasiyyin annabi (A.S) idan kuwa ba haka ba to wanda ya hau wannan mahalli a wajen Allah sunansa fajiri fasiki komai kuwa takawarsa ta zahiri, domin ma’aunin da muke hange da shi, shi ne dai ma’aunin da Allah yake hange da shi.

Idan kuwa yana son kada wannan suna ya hau shi to kada ya sake ya hau wannan mataki sai idan annabi (A.S) ko wasiyyin annabi (A.S) ko kuma wanda wasiyyin annabi (A.S) ya ce ya hau wannan matsayin sakamakon ba a gane shi a fili koda kuwa an gan shi, sai ya mayar da mutane zuwa ga malamai masu wasu siffofin da shi ya ayyana su da kansa da shiryarwar ubangijinsa madaukaki da kuma ta annabin rahama (S.A.W).

Imam Ali (A.S) yana cewa da alkali shuraihu: Ya shuraihu ka zauna a mazaunin da babu mai zama a wurin sai annabi (A.S) ko kuma wasiyyin annabi (A.S) ko kuma tababben tsinannen mutum (al’wasa’il: babin hukunci: babi 2, h 2, shafi: 6). Kamar yadda imam sadik (A.S) yake cewa: Ku ji tsoron mulki domin shi mulki na malami ne masani da hukunci da adalci wanda yake shi ne annabi (A.S) ko kuma wasiyyin annabi (A.S) (Daga al’wasa’l: kamar na bayansa). Don haka ne ma ake fassara ma’anar malamai a irin wadannan hadisai da annabi (A.S) ko kuma wasiyyin annabi (A.S).

Amma hanzari ba gudu ba: Dayawan malamai sun tafi a kan cewa; idan aka samu wani mumini da yake karbar shawara daga malamai wadanda suke kan tafarkin manzon Allah (S.A.W) da koyarwarsa sahihiya (A.S) ya kasance yana karbar shiryarwa da yadda zai tafiyar da al’amuran al’ummarsa daga garesu to wannan ya fita daga cikin wannan tabewa kuma irin wadannan mutane ba sa ciki saboda su ma yanzu suna karkashin umarnin Allah da manzonsa da wasiyyansa da kuma malamai mabiyansu ne, kuma sun fita daga sunan fajirci, ko dagutanci.

Kamar yadda malamai suka yi fahimta ga hadisin da yake cewa duk wata tuta da aka daga (wato duk wata gwagwarmaya da ake yi) kafin bayyana Sufyani to ta dagutu ce (wato; ba halattacciya ba ce), wasu malamai sun tafi a kan hakan, amma muna iya ganin imam khomain (K) jagoran juyin musulunci a Iran a 1979, yana ganin hadisin bai hada da tutar da aka daga kuma ta kasance ba ta saba da koyarwarsu ba, sai ya kasance kenan ya halatta malamin da yake bin hanya sahihiya da sharadin ya samu lasisin wasiyyan annabi (A.S) zai iya yin wani motsi bisa sharuddan da suka gindaya. Sai ya kasance wannan kauce hanya bai hada har da shi ba. Wannan dai mas’ala ce mai girma da ta tayar da jijiyar wuya saboda santsinta da kuma wahalarta kamar yadda dai sauran mas’alolin siyasa suke. Kuma nan ba zauren karatu ba ne balle mu fadada magana.

Shin ya halatta domin gudun hukumar dagutanci mutane su zauna babu shugaba sam?

Wane irin shugabanci ne a duniya yake da inganci idan mun yi la’akari da yadda abubuwan suke wakana?

Wannan sai ku biyo mu bashi idan Allah ya sa mun samu lokaci a nan kusa…

Shin ya halatta domin gudun hukumar dagutanci mutane su zauna babu shugaba sam?

Wane irin shugabanci ne a duniya yake da inganci idan mun yi la’akari da yadda abubuwan suke wakana?



back 1 2 3 4 5 6 7 next