Kaunar Juna



F-Mafi Amfanin Taskoki

13- Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Mafi amfanin taskoki ita ce soyayyar zukata[17].

G-Mafi Dadin Abu

14-Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: cewa shi ya ji Ja’afar dan Muhammad (A.S) yana cewa; Annabi Dawud (A.S) ya tambayi Annabi Sulaiman (A.S) –yana son ya san matsayin da ya kai na hikima- sai ya ce: masa; … Wane abu ne ya fi dadi? Sai ya ce: soyayya, ita ce ruhin Allah (S.W.T) tsakaninsa da bayinsa, kai har ma doki yana dage kofatonsa ga dansa. [Imam (A.S) ya ce: sai Dawud (A.S) ya yi dariya saboda amsar da Sulaiman (A.S) ya bayar[18].

1 / 3

Falalar Abokai Da kuma Neman Yawaita (Adadin) Su

15-Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Ku yawaita yan’uwa; ku sani kowane mumini yana da ceto ranar kiyama[19].

16- daga garshi: Mutum ya yawaita yawan ‘yan’uwansa musulmi[20].

17- Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Na umarce ka da ka yi riko da ‘yan’uwan abokantaka, Ka yawaita nemansu, domin su tattali ne gun yalwa, kuma garkuwa ne gun bala’i[21].

18- Daga gareshi (A.S) ya ce: ‘Yan’uwan abokantaka a cikin mutane sun fi dukiya da ake cinyewa kuma ake gadon ta alheri, kada wani ya karanta alakarsa da dan’uwansa, kuma kada ya musanya shi da wani domin bai ga wata yalawa tare da shi ba, ko kuma ya gan shi mai karancin dukiya. Kada wani ya gafala daga makusancinsa na jini da zai gan shi da wata bukata sai ya biya masa ita da wani abu da ba zai cutu ba don ya ciyar masa da shi, kuma ba zai amfane shi ba idan ya rike shi[22].

19. Daga gareshi (A.S) ya ce: wanda ba shi da aboki ba shi da ajiya[23].

20. Imam Ja’afar Sadik (A.S) yana cewa: ku yawaita abokai a wannan duniya; ku sani su suna da amfani a duniya da lahira, amma a duniya ta hanyar bukatu da suke biya muku ita, amma a lahira ku sani ‘yan jahannama sun ce: “ba mu da mai ceto ko wani aboki mai kauna” [24].

21. Imam zainul abidin (A.S): kada ka yi gaba da wani koda kuwa kana tsammanin ba zai cutar da kai ba, kada kuma ka yi karancin abokantakar wani koda kuwa kana tsammanin ba zai amfane ka ba, domin kai ba ka sani ba yaushe ne zaka kaunaci son (taimakon) abokinka, kuma ba ka sani ba yaushe ne kake tsoron (sharrin) makiyinka. kuma kada wani ya kawo maka kuka sai ka karbi kukansa ka share masa hawayensa koda kuwa ka san shi makaryaci ne[25].



back 1 2 3 4 5 6 7 next