Kaunar Juna



Kaunar Juna

1 / 1

Imani Da Sabawa

Kur’ani

“Ku yi riko da igiyar Allah gaba daya kuma kada ku rarraba, kuma ku tuna ni’imar Allah gareku yayin da kuka kasance makiya sai ya hada zukatanku, sai kuka wayi gari kuna ‘yan’uwa, kuma kun kasance a gefen wuta sai ya tseratar da ku daga gareta, haka nan Allah yake bayyana muku ayoyinsa ko kwa shiriya” [1].

“Shi ne wanda ya taimake ka da nasararsa da kuma muminai. kuma ya hada zukatansu, da ka ciyar da abin yake cikin kasa gaba daya da ba ka iya hada tsakanin zukatansu ba, sai dai Allah ne ya hada tsakaninsu, hakika shi mabuwayi ne mai hikima” [2].

“Hakika muminai ‘yan’uwa ne ku yi sulhu tsakanin ‘yan’uwanku, kuma ku ji tsoron Allah ko a yi muku rahama” [3].

“Idan suka tuba suka tsayar da salla suka bayar da zakka, to fa ‘yan’uwanku ne na addini, kuma muna rarrabe ayoyi ga mutanen da suke sani”[4].

Hadisai:

1. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Hakika Allah madaukaki ya sanya musulunci tafarki mai hasken tutoci, mai hasken manarori, a cikinsa ne zukata suke haduwa, kuma a kansa ne ‘yan’uwa suke ‘yan’uwantaka[5].

2. Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Hakika ruhin imani daya ne da ya fita daga abu daya da yake warwatsuwa cikin jikunkunan mutane mabambanta, kuma a kansa ne suke haduwa, kuma da shi ne suke son juna[6].

3. Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Muminai suna sabawa kuma ana sabawa da su, kuma ana zuwa mazauninsu[7].



1 2 3 4 5 6 7 next