Kaunar Juna



4. Mas’alolin Ali dan Ja’afar: daga Ali dan Ja’afar ya ce: Na ce da Abul Hasan (A.S): Wane ne ya fi mu son addininsa? Sai ya ce: “Mafi tsananinku son sahibinsa” [8].

1 / 2

Kimar Soyayya

A-Alamar Karfin (Kaifin) Hankali

5- Daga Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: Asasin hankali bayan imani da Allah madaukaki shi ne neman soyuwa wajen mutane[9].

6- Daga gareshi (S.A.W): Neman soyuwa a wajen mutane ita ce rabin hankali[10].

B- Rabin Addini

7- Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Soyayya rabin addini ce[11].

C- Kusanci Mai Amfanuwa

8- Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Soyayya ita ce dayan makusanta biyu[12].

D-Mafi Kusancin Kusanci

9- Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Mafi kusancin kusanci shi ne soyayyar zukata[13].

10- Daga gareshi: Da yawa makusanci ya fi nisa fiye da manisanci, kuma da yawa manisanci ya fi kusanci fiye da makusanci[14].

E-Asalin Kusancin (‘Yan’uwantakar Jini)

11- Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Da yawa (zaka samu) wani dan’uwa da ba mahaifiyarka ce ta haife shi ba[15].

12- Daga gareshi: Abokinka shi ne dan’uwanka na uwa daya uba daya, ba duk wani dan’uwanka na uwa daya uba daya ba ne yake zama abokinka ba[16].



back 1 2 3 4 5 6 7 next