Sabuban Soyayya



g- Iyawa

92. Imam Ali (A.S) ya ce: Wanda iyawarsa ta kyautata, sai jagoransa ya so shi[52].

h- Ziyara

93. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ziyara tana shuka kauna[53].

i- Sadar Da Zumunci

94. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: sadar da zumunci yana wajabta soyayya[54].

j- Yada Sallama

95. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ba zaku shiga aljanna ba har sai kun yi imani, ba kuma zaku yi imani ba har sai kun so juna, shin ba na shiryar da ku ga wani abu ba da idan kuka yi shi zaku so juna? Ku yada sallama a tsakaninku[55].

K- Tausasa Magana

96. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Ka saba wa kanka taushin magana, da yada sallama, sai masu kaunarka su yawaita, masu kin ka su karanta[56].

l- Kyauta

97. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: kyauta tana haifar da kauna, tana sabunta ‘yan’uwantaka, tana kawar da kiyayya[57].

M- Yin Hannu

98. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ku yi hannu da juna sai kiyayya ta tafi daga zukatanku[58].

N- Nasiha

99. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: nasiha tana haifar da soyayya[59].

O- Zargin Hankali

100. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: kada ka dora wa jahili laifi sai ya ki ka, ka dora wa mai hankali sai ya so ka[60].

P- Sujjada Tsakanin Kiran Salla Da Ikama

101. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Imam Ali (A.S) ya kasance yana gaya wa sahabbansa: wanda ya yi sujada tsakanin kiran salla da ikama sannan sai ya fada a sujadarsa: “Ubangiji gareka na yi sujada ina mai kaskatar da kai mai tsoron ka, kaskantacce a gabanka” to Allah madaukaki zai ce: Ya ku mala’ikuna, na rantse da buwayata da girmana sai na sanya sonsa a zukatan bayina muminai, da kwarjininsa a zukatan munafikai[61].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next