Sabuban Soyayyah- Ladabi
66. Imam kazim (A.S): Kada ka kawar da jin kunya tsakaninka da dan’uwanka, ka wanzar da ita; domin idan ta tafi, kunya ta tafi, kuma wanzuwar jin kunya shi ne wanzuwar kauna[25]. i- Kauna
67. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Da kaunar juna ne ake karfafa soyayya[26]. 68. Imam Muhammad Bakir (A.S) ya ce: Wani mutumin kauye daga banu tamim ya zo wajen Annabi (S.A.W) sai ya ce masa: yi mini wasiyya. Ya kasance daga abin da ya yi masa wasiyya shi ne: ka soyu zuwa ga mutane zasu so ka[27]. j- Kaskanda Kai
69. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: soyayya ita ce sakamakon kaskanda kai[28]. K- Cikawa Da Alkawari
70. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: cika alkawari yana kawo shakuwa da juna[29]. l- Adalci
71. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: adalci yana kawar da sabani, yana kuma kawo shakuwa da juna[30]. 72. Daga gareshi (A.S) ya ce: Adalci yana dawwamar da soyayya[31]. 73. Daga gareshi (A.S) ya ce: Mai adalci yana da yawan masoya da masu kauna[32]. m- Gaskiya
74. Imam Ali (A.S) ya ce: mai gaskiya yana samun abubuwa uku: kyautata amintuwa da shi, da sonsa, da kuma jin kwarjininsa[33]. n- Tausasawa
75. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: wanda dabi’arsa ta tausasa, to sonsa ya wajaba[34].
|