Sabuban Soyayya



51. Daga gareshi (A.S) ya ce: hakika rayuka idan suka samu jituwa sai su saba[7].

52. Daga gareshi (A.S) ya ce: mai hankali yana sabo da irinsa ne[8].

53. Daga gareshi (A.S) ya ce: Babu mai soyayya da ashararai sai irinsu[9].

54. Amali na Dusi daga Sadir na ce da Abu Abdullahi (A.S) ni ina haduwa da mutumin da bai taba gani na ba, ni ma ban taba ganinsa ba kafin ranar haduwarmu sai in so shi so mai tsanani, idan na yi masa magana sai in samu shi ma yana kan irin abin da nake a kai, kuma ya gaya mini shi ma yana jin irin abin da nake ji gareshi. Sai ya ce: ka yi gaskiya ya kai Sadir, ka sani hakika sabawar zukata nagari[10] idan sun hadu koda kuwa ba su nuna kauna ba da zukatansu kamar saurin cakudar digon ruwan sama ne da yake sauka kan ruwan koramu, kuma hakika nisantar zukatan fajirai idan sun hadu koda ba su nuna soyayya da zukatansu ba, kamar nisantar dabbobi ne daga tausasawa koda kuma sun dade a kan wajen makiyaya[11] daya[12].

55. Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya gaya wa Umar dan yazid: kowane abu yana da wani abu da yake hutawa wajensa. Hakika mumini yana hutawa ne wurin dan’uwansa mumini kamar yadda tsuntsu yake hutawa wurin irinsa, ko ba ka ga haka ba ne? [13]

 

3 / 3

Imani Da Aiki Na Gari

Kur'ani:

“Wadannan da suka yi imani suka kuma yi aiki na gari da sannu Ubangiji zai sanya musu soyayya” [14].

Hadisai:

56. Imam Ali (A.S) ya ce: Na ce ya ma’aikin Allah ba ni labarin fadin Allah madaukaki “da sannu Ubangiji zai sanya musu soyayya”? sai ya ce: ya Ali (A.S) soyayya gun Allah da mala’iku da kuma cikin zukatan muminai. Ya Ali, hakika Allah madaukaki ya ba wa muminai uku: kauna da soyayya da kwarjini a cikin zukatan muminai[15].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next