Wuce Gona Da Iri



Daga wajensa (a.s) ya ce: “Idan la’ana ta fita daga ma’abucinta za ta yi yawo tsakaninsa da wanda aka la’antar, idan ta samu wajen zama shi kenan idan kuwa ba ta samu ba sai ta koma wajen mai ita, shi ya fi dacewa da ita. Don haka ku guji la’antar mumini don kada ta fada kanku[17]”.

g) – Cin Naman Mumini

Daga ciki har da ambaton mumini a bayansa da abin da ba ya so, da kuma bayyanar da aibinsa da ya boye, shi ne abin da ake kira da ‘giba’ (cin nama) da Alkur’ani ya bayyana haramcin a fili, inda ya siffanta shi da cin naman mamaci “…kuma kada sashenku ya yi gibar sashe. Shin, dayanku na son ya ci naman dan’uwansa yana matacce? To, kun ki shi…[18]”.

Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Wanda ya fadi wani abu kan mumini daga abin da idanuwansa suka gani ko kuma kunnuwansa suka ji, to yana daga cikin wadanda Allah Madaukakin Sarki Ya fadi dangane da su cewa: Lalle ne wadanda ke son alfasha ta watsu ga wadanda suka yi imani, suna da azabamai radadi[19]”.

Cikin wasiyyar Manzon Allah (s.a.w.a) ga Abu Zar, yana cewa: “Ya Aba Zar! Ina gargadinka da giba, saboda giba ta fi zina tsanani”, sai na ce: Saboda da me Ya Rasulallah? Sai ya ce: Saboda mutum ya kan yi zina ya kuma tuba Allah Ya karbi tubansa, ita kuwa giba ba a yafe ta har sai wanda aka yi ta a kansa ya yafe. Ya Aba Zar, zagin musulmi fasikanci ne, kisansa kuwa kafirci, cin namansa kuwa na daga cikin sabon Ubangiji, haramcin dukiyarsa tamkar haramcin jininsa ne. Sai na ce: Ya Rasulallah, mece ce giba? Sai ya ce: Ambatonka ga dan’uwanka da abin da ba ya so, sai na ce Ya Rasulallah, ko da yana da wannan abin da aka ambata din? Sai ya ce: Ka san cewa idan har ka ambace shi da abin da yake da shi ne ka ci namansa (giba), idan kuwa ka ambace shi da abin da ba shi da shi ne, ka zalunce shi[20]”.

Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Wanda ya yi mu’amala da mutane bai zalunce su ba, ya kuma yi magana da su bai musu karya ba sannan ya yi musu alkawari bai saba musu ba, yana daga cikin wadanda gibansu ta haramta, kuma mutumcinsa ya cika, adalcinsa ya bayyana sannan ‘yan’uwa da shi ya wajaba[21]”.

Malaman fikihu sun gibar fasiki mai bayyanar da fasikancinsa a fili cikin gibar da ta haramta. Daga Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Idan fasiki ya bayyanar da fasikancinsa a fili, to babu haramci gare shi da kuma giba[22]”.

Abul Hasan (a.s) yana cewa: “Wanda ya ambaci wani mutum a bayan idonsa da wani abin da ke tattare da shi wanda kuma mutane suka sani bai yi gibansa ba, wanda kuma ya ambace shi a bayan idonsa da abin da yake tare da shi amma mutane ba su sani ba, ya yi gibansa, wanda kuwa ya ambace shi da abin da ba shi da shi ya kirkiri karya gare shi[23]”.

h)– Kirkirar Karya

Babu shakka kirkira karya a kan mumini zalunci ne mai girman gaske da har ya fi giba girma, an ruwaito wani ingantaccen hadisi daga Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Wanya ya kirkiri karya ga mumini ko mumina kan abin da ba ya cikin halayensu, Allah Zai tura shi cikin Dinat Khibal har abin da ya fadi ya fice, sai na ce: mene ne Dinat Khibal kuma? Sai ya ce: Diwan da zai dinga fita daga farji….[24]”.

i)- Annamimanci

Daga cikin hakan, har da annamimanci da bata alakar da ke tsakanin muminai da raba kawukansu. An ruwaito Imam Sadik (a.s) cikin wani ingantaccen hadisi yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Ashe ba zan ba ku labarin mafi sharrin cikinku ba? Sai suka ce na’am Ya Rasulallah, sai ya ce: su ne masu yawo da annamimanci, masu raba tsakanin masoya, masu sanya aibi da maras shi cikin zalunci[25]”.

Manzon Allah (s.a.w.a) cikin wasiyyar da ya yi wa Abu Zar (r.a) yana cewa: “Ya Aba Zar! Al-Kattat ba zai shiga Aljanna ba, sai na ce: Ya Rasulallah, wane ne kuma al-Kattat? Sai ya ce: “annamimi. Ya Aba Zar, annamimi ba zai taba hutawa daga azabar Allah ba a Ranar Kiyama. Ya Aba Zar, ma’abucin fuskoki da harsuna biyu a duniya zai kasance ma’abucin fuskokin biyu a wuta. Ya Aba Zar, (ka) zauna da (mutane) cikin amana, bayyanar da sirrin dan’uwanka ha’inci ne, ka nesanci hakan, ka nesanci zama da mai neman (aibin mutane)[26]”.



back 1 2 3 4 5 6 7 next