Wuce Gona Da Iri



Daga Abi Harun, daga Abi Abdillah (a.s) ya ce: “Ya gaya wa wasu mutane alhali a lokacin ina wajen cewa: Me ya sa ne kuke wulakantamu? Sai wani mutum daga Khorasan ya mike ya ce: Allah Ya tsare mu da wulakantaka ko kuma wani abu daga cikin al’amurranka, sai ya ce: Na’am, kai kana daga cikin masu wulakanta ni, sai ya ce: Allah Ya tsare ni kan in wulakantaka, sai ya ce masa: Kaiconka! Ashe ba ka ji wane alhali muna kusa da al-Juhufa ba yana ce maka: dauke ni gwargwadon mil guda, wallahi bana iya magana? Wallahi ba ka daga ko kanka gare shi ba, ka wulakanta shi, duk kuwa wanda ya wulakanta mumini ya wulakanta mu, ya kuma keta hurumin Allah Madaukakin Sarki[9]”.

d)– Kaskantar da Mumini

Daga ciki har da kaskantar da mumini ta hanyar aikata zunubi da munanan aiki, da aibata shi, hakan ma banda (batun) hana shi aikata munkari da masa nasiha da nufin hana shi aikata zunubi.

An ruwaito Imam Sadik (a.s) cikin wani ingantaccen hadisi yana cewa: “Wanda ya kaskantar da mumini da wani zunubi, ba zai mutu ba har sai ya hau shi[10]”.

Har ila yau daga gare shi (a.s) yana cewa: “Duk wanda ya zo wa dan’uwansa da abin da zai musguna masa, Allah Zai musguna masa duniya da lahira[11]”.

e)– Sanya Ido Kan Gazawar Mumini

Daga ciki har da sanya ido kan gazawar mumini da nufin cutar da shi da amfani da hakan wajen cin mutumcinsa.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Abin da zai fi nesantar da bawa daga Allah shi ne ya kasance mai sanya ido da kula da gazawar dan’uwansa da amfani da hakan wajen kaskantar da shi da cin mutumcinsa[12]”.

Daga Ishak bn Ammar yana cewa: “Na ji Aba Abdillah (a.s) yana cewa: Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Ya ku taron wadanda suka mika kai da harshensu, ba su tabbatar da imani zuwa zukatansu ba. Kada ku zargi musulmi sannan kada ku sanya ido kan sirrinsa don kuwa duk wanda ya sanya ido kan sirrinsu, Allah Zai sanya ido kansa, wanda kuwa Allah Ya sanya ido kansa, Zai tona shi ko da a cikin gidansa ne[13]”.

f)– Zagin Mumini da Bata Masa Suna

Daga ciki har da zagin mumini ko la’antarsa ko bata masa suna. An ruwaito wani hadisi daga Abil Hasan Musa (a.s) kan wasu mutane biyu da ke zagin junansu, inda ya ce: “Wanda ya fara daga cikinsu shi ne yafi zalunci, laifinsa da laifin dayan na wuyansa matukar bai nemu gafarar wanda aka zalunta ba[14]”.

Abu Ja’afar (a.s) yana cewa: “Wani mutum daga kabilar Bani Tamim ya zo wajen Ma’aiki (s.a.w.a) ya ce: ka yi min wasiyya, daga cikin abin da ya masa wasicci da shi har da cewa: Ka da ka zagi mutane, sai ka samar da kiyayya gare su[15]”.

Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Allah Madaukakin Sarki Ya halicci mumini ne daga girman daukaka da kudurarSa, duk wanda ya bata masa suna ko ya mayar masa da magana, to ya mayar wa Allah ne[16]”.



back 1 2 3 4 5 6 7 next