Ma'aunin Matsayin AlakaKo kuma wasu hukumce-hukumcen dake da alaka da ladubban zama (taro) ko kuma lakca da magana kamar buda wajen zama da wanda suka shigo ko kuma tashi tsaye don girmamawa ga wanda ya shigo, ko kuma kiransa da alkunya ko kuma kiransa da sunan da ya fi so. Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Abubuwa uku suna nuni da kaunar mutum ga dan’uwansa musulmi: zai tarbe shi da sakin fuska da murmushi a lokacin da ya hadu da shi, zai buda masa wajen zama idan ya zauna kusa da shi, sannan kuma zai kira shi da mafi kyaun sunan da yafi so[4]â€. Daga gare shi (a.s) daga Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: “Idan waninku yaso dan’uwansa musulmi zai tambaye shi sunansa da sunan mahaifinsa da sunan kabilarsa, hakika yin wadannan tambayoyi na daga cikin hakkokinsa na wajibi na abokantaka da ‘yan’uwantaka, idan kuwa ba haka ba, to sanayyarsu, sanayya ce ta wauta[5]â€. Ko kuma hukumce-hukumcen da ke da alaka da kebancewa a wajen zama.
Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Idan mutane uku suna tare, kada biyu daga cikinsu su kebance ba tare da na ukun nasu ba, saboda akwai cutarwa gare shi cikin hakan[6]â€. Haka nan za mu iya samun karin bayani na musamman a yayin da Madaukaki Sarki Ya hana abokantaka da fajirin mutum, wawa, makaryaci ko kuma neman shawarar bayi, wulakantattu mutane ko kuma fajiri, ko abokantaka da mai yanke zumunci ko kuma kaskantaccen mutum ko kuma masu rayuwa irinta almubazzaranci kuma mata, kamar yadda muka yi nuni da hakan cikin bahasi kan ababen da aka kebance su. Kamar yadda a baya bayani kan wasu daga cikin wadannan koyarwa da sauransu suka gabata yayin bayani kan wabubuwan karfafa ginin al’umma, ta yadda wasu daga cikin wadannan nasihohi sun shafi wannan alaka ne, kamar yadda yake a fili. AlakarAbokantaka ta Musamman (Amincewa)
Amma matsayi mafi girma na alaka shi ne alaka ta amicewa da ke nuni da matsayin alakar ‘yan’uwantaka ta hakika, dake da hakkoki da wajibai da suka kebanta da wannan matsayi. Za mu iya ganin siffofi na tsari da hukumce-hukumcen dake da alaka da wannan matsayi na alaka cikin wasu dokoki da ke magana kan sharuddan aboki da dan’uwan da dole ne mutum ya yi riko da su, misali hankali da takawa, amana da kiyaye sirri, taimako da rashin wofantarwa, da shirin daidaitawa, karimci, gaskiya cikin mu’amala, kiyayewa wajen aiwatar da wajibi musamman salloli, ikhlasi cikin ‘yan’uwantaka, sannan kuma dole ne wannan ‘yan’uwantaka ta kasance saboda Allah Madaukakin Sarki. A baya mun yi ishara da wasu hadisai da suka yi bayani kan wasu daga cikin wadannan siffofi cikin………….., haka nan ma’auni na farko, wato budaddiyar zuciya (tunani) lokacin da muka yi magana kan ababen da aka kebance su. Ga wasu ruwayoyi (nassosi) ma na daban:
Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Amirul Muminina (a.s) ya ce: Ba wajibi ba ne abokantaka da ma’abucin hankali ba matukar ba ka gode wa karimcinsa ba, face dai ka amfanu da hankalinsa…ka kula da munanan dabi’unsa, kada…ko da baka amfana da hankalinsa ba, to amma ka amfana da karimcinsa ga hankalinka, ka gudu dukkan guduwa daga daga wawa maras hankali[7]â€. Kuma Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “………..[8]â€.
|