Ma'aunin Matsayin AlakaNA HUDU: MA’AUNIN MATSAYIN ALAKA
Amma dangane da mahanga ta hudu wacce ita ce matsayin alaka, a baya mun ce, duk da cewa mahangar Musulunci ya yi amanna da daidaituwa (rashin nuna bambanci) cikin alaka, to amma saboda wasu dalilai na zamantakewa sun nuna cewa wannan alaka tana da wasu matakai, su ne kuwa guda uku: a)- Alakar Girmamawa ta gaba daya. b) – Alakar abokantaka ta gaba daya. c) – Alakar abokantaka ta musamman (amincewa). AlakarGirmamawa ta Gaba Daya
Amma dangane da alaka ta girmamawa da zamantakewa ta gaba daya, muna iya ganin karin bayani kan tsari da hukumce-hukumcenta cikin abubuwan da muka ambata a fadaddiyar zuciya na rayuwa cikin mutane, da kuma abubuwan da aka ambata a ka’idar kauna, girmamawa da zama da mutane mai kyau. Kazalika ka’idar hadiye fushi da ka’idar kyautatawa da sauransu da za a yi cikakken bayaninsu nan gaba. Wadannan karin bayani, ko da yake suna da alaka ta kai tsaye ne da wadannan ka’idoji da asasai da muka yi ishara da su a baya, to amma duk da haka suna nuni da tafarki na gaba daya na alakar zamantakewa da ke nuni da wajibcin samar da alaka ta girmamawa tsakanin dukkanin al’umma, face sai cikin ababen da aka kebance su da muka yi ishara gare su a baya. AlakarAbokantaka Ta Gaba Daya
Daga hadisan da muka ambata a baya wajen matsayin alaka, ana iya cewa alaka ta abokantaka ta gaba daya tana nufin alakar da ta dara alakar girmamawa, da za ta kare a yanayi na abokantaka ta rayuwa, ko dai ta hanyar aikin neman rayuwa, ko tafiye-tafiye ko makwabtaka ko kuma abokantaka ta karatu ko sana’a da dai sauran dalilai. A irin wannan yanayi yana da kyau mutum ya tsaya bisa iyakokinta ta dabi’a da mutum zai iya samun abubuwan amfaninsa, kamar yadda yazo cikin wata ruwaya cewa: “Page 35……[1]â€. Abin so shi ne cudeni in cude ka cikin wadannan ababen amfani da jin dadi “ka ba su abin da suka baka na sakin fuska da dadadan maganganu[2]â€. Za mu iya samun cikakken bayani kan hukumce-hukumcen wannan alaka cikin hukumce-hukumcen da suka shafi abokantaka ta tafiya da ladubbanta, misali cikin babuka na 30-34 daga babukan ladubban tafiya hajji da sauransu[3]. Ha kaza lika cikin wasu hukumce-hukumcen da ke da alaka da mu’amala da ma’aikata da yaran gida ko kuma hukumce-hukumcen da ke da alaka da ladubban koyo da koyar da karatu da suka shafi batun abokantaka.
|