Daurewa Rayuwar Tare



Sai dai duk da hakan, za mu iya ganin Ahlulbaiti (a.s) suna jaddada muhimmancin magana da kalami a wajen da ya dace da zai haifar da sakamako mai kyau.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Magana kan gaskiya ya fi alheri kan shiru kan karya[22]”.

Daga Ali bn Husain (a.s) yana cewa: “Kyakkyawar magana ta kan kyautata dukiya, da kara arziki, ….cikin ajali, da kara soyayya cikin iyali, da kuma shigar (da mutum) Aljanna[23]”.

A cikin wata wasiyya da ya yi wa Abu Zar (r.a), inda ya bayyana ingantaccen ma’auni tsakanin magana da shiru, Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: “Ya Aba Zar! Mai zikiri cikin gafalallu tamkar mayaki ne saboda Allah cikin ma’abuta gudu (yayin yaki). Ya Aba Zar! Zama da mutum salihi ya fi kadaitaka, amma kadaitaka ta fi zama da mugun mutum, zancen alheri (gaskiya) ya fi zama shiru, amma shiru ya fi mugun magana. Ya Aba Zar! Ka nesanci tsoma baki cikin maganar da ba ta shafe ka ba, magana gwargwadon bukatarka tai she ka. Ya Aba Zar! Ya ishe mutum ya zama makaryaci idan zai yi magana kan dukkan abin da ya gani. Ya Aba Zar! (Ka sani) babu abin da ya dace a tsare shi a gidan yari na tsawon lokacin kamar harshe. Ya Aba Zar! Hakika Allah Yana nan a gaban harshen duk wani mai magana, don haka mutum ya ji tsoron Allah ya kuma san abin da zai fadi[24]”.

An ruwaito Abu Abdillah (a.s) yana ce wa wani mutum da ya yi maganganu masu yawa a gabansa cewa: “Ya kai wannan mutum, ka wulakanta magana da rage ta, hakika Allah Bai aiko manzanninSa ………………., face dai ya aiko………….[25]”.

f)– Hadiye Fushi da Hakuri Kan Hassada

Daga cikin wadannan abubuwa har da iko da kame kai yayin fushi da kuma shu’urin son ramuwa da daukan fansa, musamman idan mutum ya kasance shi ne kan gaskiya ko kuma wanda aka zalunta, ta yadda zai iya rike kansa da amfani da hankali, hikimar da karfinsa wajen hadiye wannan shu’uri mai karfin gaske.

An ruwaito ta ingantattun hanyoyi daga Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Madalla da jaruntakar fushi ga wanda ya yi hakuri kanta, saboda girman lada (sakamako) gwargwadon girman bala'i ne, lalle Allah ba Zai so wata al’umma ba face sai ya jarrabe ta[26]”.

Haka nan an ruwaito Imam Sadik (a.s) yana cewa: “(Imam) Ali bn Husain (a.s) ya kasance yana cewa: ……………[27]”.

Allah Madaukakin Sarki Ya siffanta bayin na gargaru da wannan siffa cikin fadinSa: “Masu hadiye fushi kuma masu yin afuwa ga mutane”.

Cikin wata wasiyya da ya yi wa Ali (a.s), Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: “Ya Ali! Ina maka wasicci da wata wasiyya da lalle ka kula da ita, za ka kasance cikin aminci matukar ka kiyaye wannan wasiyya tawa. Ya Ali! Duk wanda ya hadiye fushi alhali yana da karfin azabtar da wannan ya bata masa rai……[28]”.



back 1 2 3 4 5 6 7 next