Daurewa Rayuwar Tare3 – Hadiye Fushi da Rayuwar Tare
Za mu iya ganin misali da karin bayani da Allah Madaukakin Sarki da Ahlulbaiti (a.s) suka yi a fagen rayuwa da alaka ta zamantakewa, da ke nuni da matsayin wannan ka’ida mai muhimmancin gaske cikin alaka ta zamantakewa a mahangar Musulunci: a)– Kyautata Abokantaka
Na farko shi ne kyautata abokanta, da hakuri da abokan zama da na kurkusa da sauransu da a mafi yawan lokuta mutum ya kan samu kansa cikin alaka ta zamantakewa da su. Daga Abil Rubai'i al-Shami yana cewa: “wata rana na tafi wajen Abi Abdillah (a.s) alhali gidan na cike da mutanen gidan, cikinsu akwai mutanen Khorasan, da Sham da sauran gurare, don haka ban samu wajen da zan zauna ba. Abu Abdullah (a.s) yana zaune ya jinginu sai ya ce: “Ya ku ‘yan shi’an Iyalan gidan Muhammadu, ku sani, ba ya daga cikinmu wanda ba zai iya rike kansa ba yayin fushi, da kuma wanda ya gagara kyautata zama da wanda ya zauna da shi, da dabi’u na kwarai ga wanda ya yi masa haka, da raka wanda ya raka shi, da makwabtaka da wanda ya yi makwabtaka da shi, da cin abin da wanda ya ci abinci da shi[1]â€. Abu Ja’afar (a.s) ya ce: “Ba a kula da wanda ya dauki wannan tafarki idan ba shi da wasu siffofi uku: tsantsainin da zai hana shi sabon Allah, da juriyar da za ta sanya shi hadiye fushinsa da kuma kyakkyawar zama da wanda ya zauna da shi[2]â€. A nan ma Ahlulbaiti (a.s) sun ambaci wasu ababe da suke nuni da kyakkyawan zama na abokantaka. Kamar abin da aka ruwaito da Imam Sadik (a.s) cikin littafin al-Mahasin: “Ba nagarta ba ne mutum ya yi magana kan abin da ya fuskanta a tafiya na alheri ko sharri[3]â€. Misali rashin samun damar jin halin abokin tafiya bayan rabuwa; daga Mufaddhal bn Umar yana cewa: “Wata rana na tafi wajen Abi Abdillah (a.s) sai ya ce min: “wane ne wannan abokin nakaâ€, sai na ce masa: wani mutum ne daga cikin ‘yan’uwana, sai ya ce: “me yake aikatawa?â€, sai na ce: tun da na shigo ban san halin da yake ciki ba. Sai ya ce min: “Ashe ba ka san cewa duk wanda ya kasance tare da wani mumini na tsawon taku arba’in, Allah Zai tambaye shi Ranar Kiyama?â€. Haka nan tambayar wanda mutum ya zauna da shi dangane da sunansa, alkunyarsa, nasabarsa da kuma yadda ya kasance, da karhancin kin yin hakan, sai dai kuma hakan ba tare da kokarin jin kwakwaf da cutar da wanda ake tambayar ba. Mai yiyu wannan hadisin da Aliyu bn Husain (a.s) ya ruwaito daga kakansa Manzon Allah (s.a.w.a) zai iya yin karin haske kan wadannan alamomi da misalai na wannan batu. An ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a) cewa wata rana ya gaya wa wadanda suke tare da shi cewa: “Shin kun san mece ce gazawa? Sai suka ce: Allah da ManzonSa ne suka fi sani. Sai ya ce: Gazawa uku ne: waninku ya shirya abinci don abokinsa amma sai ya saba masa ya ki zuwa, ta biyu, waninku ya zauna tare da wani mutum yana son ya san shi wane ne daga ina yake, amma su rabu ba tare da ya san hakan ba, na uku…… Abdullah bn Amru bn al-As ya ce: ya ya haka zai kasance Ya Manzon Allah? Sai ya ce:……….[4]â€. An bayyana wadannan abubuwa uku da ‘jafa'i’ cikin wani hadisi na daban da Imam Bakir (a.s) ya ruwaito daga kakansa Manzon Allah (s.a.w.a) inda yake cewa: “Abubuwa uku suna daga cikin jafa'i: mutum ya zauna da wani mutum amma bai tambaye shi sunansa da alkunyarsa ba, kuma ya gayyaci wani mutum cin abinci amma ya ki amsa masa gayyatar ko kuma ya amsa masa amma ya ki ci da kuma mutum ya fada wa iyalinsa (matarsa) ba tare da wasa ba[5]â€.
|