Matsayin Budaddiyar ZuciyaDaga Al-Kasim bn al-Rubai’ ya ce: Na ji Abi Abdillah (a.s) cikin wasiyyar al-Mufadhdhal yana cewa: “Babu mutane biyun da za su kaurace wa junansu face sai guda daga cikinsu ya cancanci bara’a da la’ana, mai yiyuwa ne ma dukkansu biyu su cancanci hakanâ€. Sai Mu’utab ya ce masa: Ya shugabana! Hakan ga wanda ya yi zalunci kenan, to shi kuma wanda aka zalunta fa? Sai ya ce: “Saboda bai kirayi dan’uwansa zuwa ga kyautata alaka ba, kuma…., lalle na ji Mahaifina (a.s) yana cewa: “Idan wata husuma ta shiga tsakanin mutane biyu, har guda ya ci zalin guda, to wanda aka zaluntar ya tafi wajen wanda ya yi zaluncin ya ce masa; Ya dan’uwana ni ne na yi zalunci don dai ya kawo karshen kauracewa juna da ke tsakaninsu. Lalle Allah Mai hukumci ne da adalci, zai karbi hakkin wanda aka zalunta daga wajen wanda ya yi zaluncin[7]â€. Haka nan daga wajensa (a.s) yana cewa: “Mahaifina ya ce: Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Babu wasu musulmi da za su kaurace wa junansu na kwanaki uku ba su yi sulhu ba face sai sun fita daga Musulunci, babu walicci tsakaninsu. Duk kuwa wanda ya rigayi magana ga dan’uwasa to zai kasance na farkon shiga Aljanna ranar hisabi[8]â€. Daga ciki har da: abin da aka ruwaito na wajibcin karbar uzuri daga sauran mutane a duk lokacin da suka bayyanar da kuskurensu da kuma neman gafara, wanda hakan na nuni da muhimmancin ci gaba da wanzuwar alakar da ke tsakani da kuma rufe duk wata kafa ta kauracewa juna. Karin bayani (kan hakan) zai zo yayin da ake karin bayani kan kyautatawa da mafi daukakan hannu. b)- Kebantattun Al’amurra
Baya ga wadannan abubuwa da suke jaddada muhimmanci samar da budaddiyar zuciya wajen alaka ta zamantakewa, za mu iya ganin cewa Musulunci ya kebance wasu al’amurra da sanya katanga a kansu, lamarin da a bangare guda yana iya zama cikamaki, a bangare guda kuma jaddadawa. Saboda kamar yadda kebancewa yake nuni da fitar abin da aka kebance din daga hukumcin abin da aka kebance daga cikinsa, haka nan kuma yana nuni da hada dukkan sauran abubuwan da suka saura daga cikin abin da aka kebance cikin hukumci, kamar yadda yake a fili. A baya, yayin da muke magana kan mahanga ta hudu na wannan nazariyya mun yi nuni da wasu daga cikin abubuwan da aka kebance cikin alakar zamantakewa ta gaba daya. A nan za mu yi nuni ne kawai ga wadannan abubuwan kebancewa a yanayi na gaba daya, da za mu takaita shi cikin tafarki guda hudu masu zuwa: Nesantar Wajajen Tuhuma
Na Farko: Halayen da suke sanya tuhuma da shakku kan daya bangaren da ake alaka da shi, lamarin da ke cutar da mutumin da ke son samar da alaka ta zamantakewa tsakanin mutane da kuma zubar masa da mutumci. Daga cikinsu akwai: a)- Alakokin da suke haifar da tuhuma cikin halaye, kamar alaka da matayen banza wanda zai sanya tuhuma da shakku kan halaccin alakar, kai hatta ma da yara ko mazaje, ko kuma alaka da ma’abuta abin hannu masu jin dadi. Me yiyuwa ne asalin alakar ko kuma yanayinta ne zai haifar da irin wannan tuhuma. Akwai ruwayoyi da suka yi hani da irin wannan nau'i na alaka. Daga Abi Abdillah (a.s) daga mahaifansa (a.s), yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: zama da mutane uku tana kashe zuciya: zama da wulakantaccen mutum (maras mutumci), zance da mata da kuma zama da ma’abuta dukiya[9]â€. Har ila daga gare shi (a.s) yana cewa: “Amirul Muminina (a.s) ya ce: Duk wanda ya kai kansa wajen tuhuma, to kada ya zargi wanda ya yi masa mummunan fahimta, duk wanda ya rufe asirinsa, to zabi na hannunsa[10]â€. An ruwaito daga Abil Hasan (a.s) yana cewa: “Abu Abdullah (a.s) ya ce: Ku guji wajeje (ababen da za su haifar) da shakku, kada waninku ya kebance da mahaifiyarsa a kan titi, don ba kowa ya santa ba[11]â€.
|