Matsayin Budaddiyar Zuciya



Na Farko: Matsayin Budaddiyar Zuciya

a)-Sauran Alamu Na Budaddiyar Zuciya

Idan muka dubi matsayin da budaddiyar zuciya take da shi a alakar zamantakewa, za mu ga cewa akwai wasu abubuwa da suke karfafa wannan matsayi.

Daga ciki akwai: jaddada batun yawaita gaisuwa (sallama) tsakanin al’umma, saboda a mafi yawan lokuta gaisuwa takan kasance mabudin kyautatuwar alaka tsakanin al’umma.

Sheikh Kulayni ya ruwaito wani hadisi da isnadinsa ke komawa zuwa ga Abi Ja’afar (a.s) inda yake cewa: “Hakika Allah Madaukakin Sarki na son yawaita gaisuwa[1]”.

An ruwaito daga Abi Abdillah yana cewa: “Yin sallama ga mutumin da ka hadu da shi na daga cikin tawali’u[2]”.

Ya zo cikin wasiyyar Manzon Allah (s.a.w.a) ga Ali (a.s) cewa: “Ya Ali! Abubuwa uku kaffara ne: yin sallama, ciyar da abinci da kuma sallar dare alhali mutane suna barci[3]”.

Daga ciki akwai kuma: jaddada kan cewa daga cikin siffofin mumini har da ya kasance mutum ne mai son mutane sannan su ma su so shi, hakan kuwa ba zai samu ba face ta hanyar kyakkyawar mu’amala da sakin fuska.

An ruwaito Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Mafi daukakanku shi ne wanda ya fi ku kyawawan halaye,…., wanda yake janyo mutane gare shi su ma suke janyo shi….[4]”.

Daga ciki akwai: Abin da yazo na haramcin kaurace wa juna tsakanin musulmi, wanda wannan hukumci ya yi daidai da batun budaddiyar zuciya wajen mu’amala, don kuwa daga wannan haramci, ko da kuwa guda daga cikin mutanen biyu shi ne wanda aka zalunta, za mu iya fahimtar tafarkin Musulunci da ke nuni da wajibcin barin kofar alaka tsakanin mutane a bude.

An ruwaito Abi Abdillah yana cewa: “Babu alheri cikin kauracewa[5]”.

An ruwaito daga Abi Ja’afar (a.s) cewa: “Babu wasu muminai da za su kaurace wa junansu sama da kwanaki uku face na barranta daga gare su a kwana na ukun”, sai aka ce masa, hakan ga wanda ya yi zalunci kenan, to shi kuma wanda aka zalunta fa (mene ne laifinsa)? Sai ya ce: “Me zai hana shi wanda aka zalunta tafiya wajen wanda ya zalunce shi, ya ce masa: ni ne nake da laifi don dai su shirya[6]”.



1 2 3 4 5 6 next