Adalci Da Daidaitawa



Daga gare shi (a.s) yana cewa: “Ya isa ya zamanto aibi ga mutum ya fahimci aibin mutane da zai sanya shi rufe ido kan lamurran kansa, ko kuma ya aibanta mutane kan wani abin da yake tattare da shi da zai iya mai da shi ga waninsa ba, ko kuma ya cutar da abokin zamansa da abin da bai shafe shi ba[20]”.

d) – Fadin Alheri Kan Mutane

Daga ciki har da fadin alheri kan mutane gwargwadon abin da mutum yake so a fadi kansa, da suka hada da kyakkyawan zato da daukan maganganu da ayyukan mutane bisa mafi kyaun fuska (zato), da kuma godiya da yabonsu.

Daga Abi Ja’afar (a.s) cikin fadin Allah Madaukakin Sarki cewa: “Ku fadi alheri kan mutane” yana cewa: “Ku fadi dangane da mutane abin da kuka fi a fadi dangane da ku[21]”.

Dukkan wadannan abubuwa za su iya kasancewa karkashin babin adalcin mutane ga kawukansu.


[1] . Wasa’il al-Shi’a 11:342, hadisi na 1.

[2] . Wasa’il al-Shi’a 11:342, hadisi na 3.

[3] . Wasa’il al-Shi’a 11:342, hadisi na 4.

[4] . Wasa’il al-Shi’a 11:343, hadisi na 1.

[5] . Wasa’il al-Shi’a 11:345, hadisi na 5.



back 1 2 3 4 5 next