Adalci Da Daidaitawa



Daga Abdillah bn Sanan yana cewa: “Na ji Aba Abdullah yana cewa: Duk wanda ya taimaki wani azzalumi wajen zaluntar wanda aka zalunta zai ci gaba da zaman cikin fushin Ubangiji har sai ya janye wannan taimako nasa[5]”.

Daga Amirul Muminina (a.s) yana cewa: “Azzalumi daga cikin mutane na da wasu alamu uku: zai zalunci wanda ke samansa da sabo, wanda ke kasansa kuma da gabala zai kuma bayyanar wa al’umma da zalunci[6]”.

Daga Aliyu bn Husain (a.s) cikin wani hadisi yana cewa: “Ina gargadinku da zama da masu sabo da kuma taimakon azzalumai[7]”.

Daga Ja’afar bn Muhammad daga Iyayensa (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: A Ranar Kiyama wani mai kira zai yi kira: ina masu taimakon azzalumai, da wanda ya ba su tawada, ko kuma ya kulle musu jaka, ko kuma ya mika muku alkalami? Ku tayar da su tare da su[8]”.

d)– Yarda da Zalunci da Shiru Kansa

Kamar yadda ya haramta mutum ya aikata zalunci da kansa, haka nan ya haramta gare shi ya yarda da kuma yin shiru kan zalunci.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Mai aikata zalunci da mai taimaka masa da kuma wanda ya yarda da hakan ‘yan’uwan juna ne (wajen aikata zalunci)[9]”.

Daga gare shi (a.s) yana cewa: “Duk wanda ya yarda (uzuri) da zaluncin mai zalunci, Allah Zai dora masa wanda zai zalunce shi a kansa, idan kuma ya yi addu’a ba za a karba ba, Allah ba Zai saka masa kan zaluncin da aka yi masa ba[10]”.

Daga gare shi (a.s) yana cewa: “Duk wanda ke fatan wanzuwar azzalumai, to lalle ya so ya ci gaba da sabawa Allah[11]”.

Misdakin Adalci da Daidaitawa Tsakanin Mutane

A bangaren adalci da daidaitawa mutum ga sauran mutane, za mu ga Ahlulbaiti (a.s) suna mana nuni da wasu abubuwa da ke tabbatar da hakan, baya ga abin da muka yi ishara da shi na daga ‘son mumini ga dan’uwansa mumini abin da yake so wa kansa’:

a)– Sakayya da Alheri

Daga cikin hakan har da sakayya da alheri da abu mai kyau da aka yi wa mutum da kamansa ko kuma wanda ya fi shi, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya ke fadi cikin littafinSa mai tsarki: ﴾ هَلْ جَزَاء الإحْسَانِ إلا الإحْسَان ﴿ “Shin, kyautatawa na da wani sakamako? Face kyautatawa[12]”.



back 1 2 3 4 5 next