Rantsuwa Da Wanin Allah



Saboda haka tare da kula da wadannan hadisai da muka kawo ta yaya za a ce Manzo ya yi hani a kan ranstuwa da annabawan Allah da waliyyai masu girma da daukaka?

2-Wani mutum ya zo wa Ibn Umar ya ce da shi ina rantsuwa da ka’aba, sai ya ce da shi a a sai dai ka rantse da ubangijin Ka’aba, domin kuwa Umar ya yi rantsuwa da babansa sai Manzo (s.a.w) ya ce kada ka yi rantsuwa da babanka, domin kuwa duk wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah ya sanya wa Allah abokin tarayya.

A cikin wannan hadisi abubuwa guda uku ne suka zo kamar haka:

A- Wani mutum ya zo wajen Ibn Umar ya yi ranstuwa sai Ibn Umar ya hane shi da yin irin wannan rantsuwa.

B- Umar ya yi rantsuwa a gaban Manzo sai ya hane shi da irin wannan ranstuwa.

C- Maganar Manzo wacce take cewa duk wanda ya yi ranstuwa da wanin Allah ya yi shirka.

Abin da yake muhimmi a wajenmu a nan shi ne kashi na biyu da na uku. Domin kuwa Ijtihadin Ibn Umar da ya yi dangane da wanda ya zo wajensa yana rantsuwa da Ka’aba hujja ne a gare shi ba hujja ne a wurimmu ba. Abin da yake muhimmi shi ne tattaunawar Manzo tare da Umar.

Amma dangane da hanin Manzo (s.a.w) da ya yi wa umar lokacin da ya yi ranstuwa da babansa, wannan ya auku ne sakamaon cewa baban Umar ya kasance mushirki ne, yin ranstuwa da mushiriki kuwa ba shi da wani matsayi, sannan kuma yana nuni ga girmama itakanta shirkai.

Amma menene abin da Manzo ya yi hani a kansa a matsayin wata ka’aida ta baki daya?

Shin yana nufin duk wani nau’i na rantsuwa da wanin Allah ko kuwa ranstuwa da irin “Lata da Uzza” wadanda suka kasance gumanka larabawa na jahiliyya, wanda zuwa wancan lokaci akwai sauran tunanin ire-iren wadannan abubuwa na bautar gumama a cikin kwakwalan musulmai, ta yadda wani lokaci ba tare da sun ankara ba sukan yi rantsuwa da su.

Saboda haka alamomin suna nuna cewa Manzo ba ya yi hani ba ne ga dukkan rantsuwa da wanin Allah, kawai ya yi hani ne da rantsuwa da gumaka da makamantansu, domin kuwa a wani hadisin ga abin da Manzo (s.a.w) yake cewa:

“Duk wanda ya yi ranstuwa sai ya ambaci Lata da Uzza a cikin rantsuwarsa, to ya ce “La’ilaha Illallah”. [15]

Wannan hadisi idan aka hada shi da hadisai guda biyu da suka gabata, zai bayyanar mana da cewa zuwa wannan lokaci akwai sauran al’adun jahiliyyana bautar gumaka a cikin zukatan musulmi, ta yadda wani lokaci sukan tuna irin wannan al’adu na jahiliyya, kuma har sukan yi ranstuwa da gumaka. Saboda haka Manzo (s.a.w) domin ya kawar da wannan mummunan aiki ya fadi wannan jumla, shi kuma Ibn Umar ya hada wannan hani da aka yi a kan ranstuwa da mushiriki da yin rantsuwa da abubuwa masu tsarki. Alhalin kuwa manufar Manzo shi ne yin ranstuwa da mushiriki wanda ba shi da wani matsayin da za a yi rantsuwa da shi.

Daga karshe zamu yi tunatarwa da cewa duk da cewa yin ranstuwa da wanin Allah ya halasta, amma ta fuskar alkalanci yin rantsuwa da Allah ne kawai hujja wacce zata sanya a amince da abin da mai rantsuwa yake fada. Don haka ranstuwa da wanin Allah ba ta wadatar wajen raba husuma da jayayya da take tsakanin wasu mutane ba, malaman fikihu kuma sun yi bayani a fili a kan hakan[16].

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Facebook: Haidar Center - December, 2012



 



back 1 2 3 4 5 6 7