Rantsuwa Da Wanin AllahImam Ali (a.s) wanda yake misali wajen tarbiyar musulunci, ya yi ranstuwa da ransa a cikin hudubobi da wasikunsa awurare da dama, sannan a wani wurin yana rantsuwa da rayukan iyayen masu saurarensa. [10] Imam Malik a cikin mu’uda yana cewa: Wani mutum ya shigo Madina yana mai karar gwamanan Yaman a wannan zamani, ya ce: Hakimin Yaman ya yanke mini hannu da kafa da dalilin cewa na yi sata, a wannan daren da ya shigo Madina ya ci gaba da ibada, ibadarsa ta janyo hankalin khalifa ya ce masa: “Ina rantsuwa da babanka darenka ba daren barawo ba neâ€.[11] Fatawawoyin Malaman Sunna A Kan Ranstuwa Da Wanin Allah Ibn Kudama a cikin littafin Mugni wanda aka rubuta shi bisa ga fikhun mazhabar Hambaliyya, yana rubuta cewa: Idan wani ya yi ranstuwa da Manzo, rantsuwarsa ta tabbata, domin kuwa Manzo yana daya daga cikin rukunnan shahadar musulunci, don haka idan ya saba, dole ne ya biya kaffara[12]. Hanafiyya suna cewa: Rantsuwa da mahaifi da ran mutum makaruhi ne. Shafi’iyya suna cewa: Rantsuwa da wanin Allah tare da nisantar shirka makaruhi ne. Daga Malik kuwa an ruwaito maganganu guda biyu ne, wanda daga cikinsu shi ne, rantsuwa da wanin Allah makaruhi ne. [13] Tare da lura da wadannan ayoyi da hadisai da muka ambata zamu iya gane hukuncin wannan rantsuwa a fili, don haka yanzu zamu yi bincike ne dangane da dalilan masu musun wannan al’amari.
|