Yin Magiya



 

Misalai Daga Hadisai

1- Hakki ne a kan Allah ya taimaki wanda ya yi aure saboda ya kiyaye kansa daga haram.[12]

Manzo (s.a.w) yana cewa: “Hakki ne a kan Allah ya taimaki wasu mutane guda uku: Mai yaki a tafarkin Allah, bawan da suka yi yarjejeniya da ubangijinsa zai ba shi wasu kudi ya ‘yanta shi, da wanda ya yi aure domin ya kiyaye kansa daga haram”.[13]

2- Shin ka san hakkin bayi a kan Allah”.[14]

Hanya ta biyu: Gaskiya ne babu wani daga cikin bayi wanda yake da hakki a kan Allah domin kuwa bayi ba wasu da wani abu ballantana su kasance suna da hakki a kan Allah, Amma Allah wanda yake mai girma ta hanyar tausayi da rahamarsa ya sanya wannan hakkin a kan bayinsa, sannan ya bayyanar da kansa a matsayin wanda bayinsa suke binsa bashin wannan hakkin. Wannan tausayi da rahama ta Ubangiji kuwa ba ta takaita da wannan ba kawai, duk da cewa shi ne mamallakin kowa da komai amma yana daukar bashi da rance daga bayinsa, kamar inda yake cewa: “Wa zai bai wa Allah kyakkyawan rance sai ya nunka masa nunki-nunki banunki mai yawa”.[15] Fahimtar gaskiyar koyarwar muslunci tana tare da bin diddigi da kulawa ta musamman.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Facebook: Haidar Center - December, 2012

 



 



back 1 2 3 4