Yin Magiya



Irin wannan addu’a ta hanya neman albarkacin manyan bayin Allah da yawa sun zo ta hanyar Imam Ali (a.s) da ‘ya’yansa tsarkaka, don haka babu bukatar kawo misalai masu yawa a kan haka.

A nan mun ga dalilai da dama wadanda suke nuni da halascin irin wannan addu’a ta hanyar hada Allah da wasu daga cikin waliyyansa. Yanzu zamu yi Bahasi don bincike a kan dalilan da wasu masu haramta irin wannan hada Allah da bayinsa na kwarai, kamar haka:

 

Babu Wani A Cikin Bayi Wanda Yake Da Hakki A Wajen Allah

Suna cewa: Rokon Alla ta hanyar wani matsayi da wani yake da shi a wajen Allah sam ba ya halatta, domin kuwa babu wani daga cikin bayi wanda yake da hakki a kan Allah.[7]

Amsa: Ana iya bayar da amsar wannan magana ta hanyoyi guda biyu kamar haka; Hanya ta farko kuwa ita ce, akwai ruwayoyi da dama wadanda suke nuni da cewa bayin Allah suna da hakki a kan Allah madaukaki, a nan zamu yi nuni ne da wasu daga cikin kamar haka:

“Taimakon Muminai wani hakki ne a kanmu”. [8]

“Alkawarin hakki a kan Allah yana cikin Attaura da Injila”.[9]

“Tseratar da muminai hakki ne a kanmu”.[10]

“Lallai hakkin karbar tuba ya wajaba a kan Allah ga wadanda suka kasance suna aikata mummuna a cikin jahilci”.[11] Shin wannan ya inganta kawai saboda mutum yana da wannan tunanin ya zamana mun yi tawilin wadannan ayoyi?



back 1 2 3 4 next