Ayyuka da Sakamako 2



Na farko: Wannan aya tana magana ne a kan sakamakon da azaba, wato duk wanda aka kama shi sakamakon ayyukansa, ba wai an kama shi ba ne sakamakon aikin wani daban, sannan wannan aya sam ba ta da alaka da bayar da lada, tare da dalilin cewa:

“Shin ba ka ga mutumin da ya juya baya ba? ya bayar da kadan ya hana mai yawa, shin yana da ilimin gaibu ne wanda yake gani da shi, ko kuwa ba shi da masaniya dangane da sahifar Musa? Da kuma rubuce-rubucen Ibrahim wanda ya cika alwkari da su. Babu wani wanda zai dauki nauyin wani. Sannan mutum ba shi da wani abu sai abin da ya aikata. Dukkan wani kokarinsa za a gan shi. Sannan za a saka masa da duk abin da ya dace. Sannan makura tana ga Ubangijinka”. [7]

Tare da kula da abin da muka yi bayani a sama zamu fahimci cewa mutum zai samu duk abin da ya cancance shi ne sakamakon ayyukansa na zunubi. Domin a cikin adabin larabci daya daga cikin ma’anonin “lamun” kamar irin wanda ya zo cikin kalmar “Lil insan” yana nuna cancanta ne, kamar yadda ya zo a cikin ayar da take cewa “Wailun lil mudaffifin” wato azaba da banu sun tabbata ga masu tauye ma’auni, domin cancantarsu da hakan sakamakon ayyukansu. Don haka wannan aya ba ta da alaka da bayar da lada, tana magana ne dangane da azaba.

Na biyu: Idan mun dauka ma cewa wannan aya tana nuni ne a kan lada da azaba, a nan akwai abubuwa guda biyu wadanda bai kamata a cakuda su wuri guda ba:

1-Rahama da azabar mutum duk sun rataye ne ga aikinsa, idan mutum ya aikata aikin kwarai zai kasance ya rabauta, idan kuwa ya zamana ya aikata mummuna zai zamana ya shiga azabar Allah. Wannan wata ka’ida ce ta Kur’ani wacce ta zo a cikin ayoyi da dama, kamae inda yake cewa: “Duk wanda ya aikata kyakkyawa don kansa, wanda kuwa ya aikata mummuna don kansa”. [8]

2- Idan mutum ya aikata kyakkyawan aiki sannan ya bayar da ladar wannan aikin zuwa ga wani wanda ya rasu, wannan mamaci zai amfana da wannan ladar.

Wannan asali guda biyu sam ba su karo da juna, ka’ida ta farko ta hade kowane mutum kuma tana magana ne yayin da mutum yake raye a duniya, sannan tana bayani ne akana bin da zai sanya mutum ya samu babban rabo a lahira ko kuwa ya tabe, amma ka’ida ta biyu kuwa tana magana ne dangane da wani abu wanda yake ya kebanci wasu ne, amma bambancin da yake tsakaninsu da kuma rashin karonsu da juna zai bayyana a cikin misalin da zamu kawo.

Mahaifi yana yi wa dansa nasiha yana cewa: Rayuwarka mai kyau da rashin kyanta yana kunshe da kokari da ka yi a cikin rayuwa, don haka fatan rayuwa mai kyau ba tare da aiki ba aikin banza ne kuma wawanci ne. Amma wannan ba yana nufin cewa ba idan wani ya ba shi kyautar wani abu kada ya karba ba, ta yadda idan ya karbi abin da aka ba shi matsayin kayauta ya kuma yi amfani da ita kamar ya saba wa maganar mahaifinsa ne, domin kuwa maganar mahaifinsa wata ka’ida ce a cikin rayuwa, amma amfana daga aikin wani mutum wani abu ne wanda yakan faru ne amma ba kodayaushe ba. Mahaifinsa yana yi masa nuni ne da ya dogara da kansa domin kuwa jin dadin rayuwa ba ya samuwa tare da ragganci da kasala. Amma wannan ba yana nufin cewa ba wani lokaci idan ta kama kada mutum ya amfana da aikin wani mutum daban ba.

 

Kalubale Na Biyu



back 1 2 3 4 5 6 next