Ayyuka da Sakamako 2



Sai Manzo (s.a.w) ya ce: Akwai gumaka a wannan wurin Sai baban Maimuna ya ce babu gumaka.

Sai Manzo (s.a.w) ya ce to cika alwakrin da ka yi wa Allah[3].

Kamar yadda muka gani a sama Manzo yana karfafawa dangane da cewa shin akwai gumaka inda za a yi wannan yankan, wannan yana nuna cewa kawai bakancen da aka yi saboda gumaka shi ne haram, domin kuwa al’adar mutanen jahiliyya ta tafi a kan wannan.

“…. Abin da kuka yanka don gumaka…. fasikanci ne”[4].

Duk mutumin da ya kula da kyau dangane da wadanda suke zuwa ziyara a wurare masu tsarki zai ga cewa, suna yin bakance ne domin samun yardar Allah a wadannan wurare, sannan suna yin yankansu ne da sunan Allah, sannan manufarsu a kan wannan shi ne, wanda aka rufe a wannan wuri ya amfana da ladar wannan abin da suka yanka, sannan mabukata su amfana da naman da aka yanka.

Fatawowin Malaman AhlusSunna

Kamar yadda ya kasance wannan al’amari wani abu ne da ya shafi fikhu, idan muka san fatawowin malam AhlusSunna dangane da wannan magana zai iya taimaka mana wajen fahimtar al’amarin, sun kasance sun kasa wannan magana zuwa gida biyu kamar haka:

Aِ-Duk lokacin da mamaci ya yi wasiyya a kan aiwatar da wani abu dukkan shugabannin mazhabobi guda hudu sun hadu a kan wajibcin aiwatar da wannan abin, kuma suna cewa mamaci yana amfana daga ayyukan wadanda suke raye.

B-Idan mutum bai yi wasiyya a kan wani abu ba, amma ‘ya’yansa ko wani na kusa da shi suna so su gabatar da wani aikin lada zuwa gare shi, dukkan malaman fikihu ban da malikiyya sun hadu a kan ingancin hakan.

1-Malaman Hambaliyya suna cewa: Duk wanda ya mutu kafin ya gabatar da hajji na wajibi, koda yana da uzuri ko kuwa ba shi da uzuri dangane da hakan, dole ne a yi masa hajji daga dukiyarsa koda kuwa bai yi wasiyya ba.



back 1 2 3 4 5 6 next