Karamomin Waliyyai



2-Yayin da wannan dan aike ya zo sai ya jefa ta a bisa fuskarsa sai ya koma yana gani”[10].

A nan babu shakka a kan cewa wanda ya warkar da annabi Yakub shi ne Allah madaukin sarki, amma kamar yadda muka yi bayani a baya, baiwar Allah da ni’imarsa suna gangarowa ne ta hanyar wasu abubuwa, ta wannan hanya ne zata isa zuwa ga sauran halittu. A nan karfin ruhin Yusuf yana da tasiri wanda ya samu ta hanyar karfin ikon Ubangiji, ta yadda ya warkar da babansa. Amma me ya sanya Yusuf ya yi amfani da wannan hanya mai sauki, amsar wannan kuwa shi ne annabawa wajen yin mu’ujiza ko sauran waliyyan Allah wajen yin karama suna amfani da hanyoyi masu sauki ne kamar haka. ta yadda kowa zai iya gane yadda suke da alaka da duniyar gaibu. Domin idan suka yi amfani da abubuwa masu wahala, mutane zasu ce ai sun yi hakan ne sakamakon wani ilimi da suke da shi.

B- Karamar Mataimaka Annabi Sulaiman

Dukkammu muna da labarin kiran sarauniyar Saba da annabi sulaiman ya yi, amma kafin ta iso wajen Sulamin (a.s) sai Sulaiman ya ce wa wadanda suke tare da shi: Ya ku taron Mutane, wa zai iya zo mini da gadon Bulkisu kafin ita da mutanenta su zo mini suna masu mika wuya”[11].

“Ni zan zo maka da shi kafin ka ta shi daga nan, kuma ina da karfin aiwatar da wannan aiki kuma ni amintacce ne a kan hakan”[12].

Ana cikin haka sai wani daga cikin mutanensa wanda yake kuma dan ‘yar uwar annabi Sulaiman ne kuma wazirinsa mai suna (Asif barkhaya) ya ce ni kafin ka rufe idonka ka bude zan zo maka da shi. Kamar yadda Allah yake cewa: “Wanda ilimin littafin yake wajensa ya ce: Zan zo maka da shi kafin ka bude idonka, lokacin da ya ganshi a tabbace a gabansa, sai ya ce wannan daga falalar ubangijina ne”[13].

A cikin fahimtar wannan aya dole ne mu kula da kyau cewa wane abu ne ya sanya wannan al’amari ya yiwu, ta yadda aka kawo wannan gadon mulki daga uwa duniya, a zahirin wannan aya ana fahimatar cewa wadannan mutane su ne suka kawo wannan gadon, amma wannan ya faru ne tare da izinin Allah (s.w.t) kuma muna iya fahimtar hakan tare da amfani da dalilan da zasu zo a nan kasa kamar haka:

Na farko: Annabi Sulaiman ya neme su da su gabatar da wannan aiki kuma yana ganin cewa suna iya yin hakan.

Na biyu: Mutumin da ya ce zai iya zuwa da wannan gado kafin Annabi Sulaiman ya mike tsaye, yana siffanta kansa kamar haka: “Ni a kan haka ina da iko kuma na amince da kaina”.

Idan har niyya da karfin wannan mutum ba su da hannu a cikin yin wannan aiki babu ma’ana ya ce: “Ni ina iya aikata wannan aiki kuma na amince da kaina”.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next